News
WHO ta bayar da gudummawar kayayyaki domin dakile cutar mashako a Jahar Kano
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayar da gudummawar kayayyaki domin tallafa wa jihar a yakin da take yi da cutar mashako.
Da yake karbar kayayyakin a Cibiyar Ayyukan Agajin Gaggawa ta Kano (EOC), Kwamishinan Lafiya na jihar, Dr. Abubakar Labaran Yusuf ya yaba wa kokarin WHO na tallafa wa gwamnati da manyan kayayyaki da nufin dakile cutar mashako a jahar Kano.
NIGERIA@63: ‘Yan Najeriya mazauna Landan sun bukaci a yi wa gwamnatin jamiyyar NNPP adalci a Kano
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai mai dauke da sa hannun Ibrahim Abdullahi, jami’in yada labarai na ma’aikatar lafiya ta jahar Kano, da ya fitar a ranar Asabar din da ta gabata.
A cewarsa, Dakta Labaran ya nuna gamsuwa da yadda tallafin ya zo a daidai lokacin da jihar ta kaddamar da wani sabon shiri a Asabar din nan na rigakafin cutar mashako, inda ya ce tuni jihar ta samu sama da alluran rigakafin cutar har fiye da miliyan daya da za a gudanar da allurar zagaye uku da ya shafi kananan hukumomi 22 a watan Oktoba, Nuwamba da Disamba.
“Isowar waɗannan kayayyakin a wannan lokacin abu ne ya dace sosai. Ina so in yi godiya ga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), musamman Mista Walter Kazadi Mulumbo, wakilin kungiyar a Najeriya.
“Baya ga cutar mashako, kungiyar na tallafa wa Kano kan wasu abubuwa da ke faruwa a jihar. Muna matukar godiya ga WHO saboda ba mu dukkan hadin kai da goyon baya da take yi”, in ji Dr. Labaran.
Daga nan sai kwamishinan ya ja hankalin jama’a da su kiyaye duk matakan kariya daga kamuwa da cutar ta mashako, inda ya nuna cewa akwai bukatar a gano cutar da wuri domin dakile yaduwarta.
Ya ba da shawarar cewa idan ana zargin wani yana da alamomin cutar, dole ne a ware shi cikin gaggawa kuma kada a bar shi ya yi cudanya da sauran mutane kuma a gaggauta kai shi asibiti domin a tabbatar ita ce ko ba ita ba ce, yana mai kira ga mutane da su sanya abin rufe hanci yayin da za su kebe wanda ya kamu da cutar, ko lokacin da za su shiga cikin taro in sun tabbatar suna dauke da cutar.
“Da zarar an tabbatar da mutum yana dauke da cutar mashako, duk danginsa da duk wadanda ya yi hulda da su dole ne a yi musu magani. Idan n yi haka, ina mai yakinin za a magance yaduwar cutar. Ina tabbatar wa jama’a cewa da tsarin da muke da shi, za mu yi rigakafin a kananan hukumomi 22.
“An gudanar rigakafin a kananan hukumomi takwas a kashi na farko, yayin da sauran 14, wadanda suka fi yawan masu fama da ke da cutar mashako, za a yi musu a kashi na biyu da aka fara yau (Asabar).
“Don haka ina rokon al’ummar da suka dace da su kai kansu da yaransu wuraren alluran rigakafi da aka tanada”, a ta bakinsa.
Cikin farin ciki Kwamishinan ya bayyana cewa daga bayanan da suke samu an samu gagarumar nasara a yaki da cutar mashako a jihar, ya kara da cewa bisa rahoton da kuma bayanan da ake da su ya nuna cewa wasu daga cikin jihohin kasar nan sun haura Kano a yawan masu cutar ta mashako.
Ya kara da cewa hakan na nuni da cewa jihar na shawo kan lamarin, yana mai alakanta wannan nasarar da jajircewar gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf da kungiyoyin da ke tallafa wa lafiya da sauran masu ruwa, yana mai fatan bisa matakan da aka dauka da yardar Allah za shawo kan matsalar.
Da yake jawabi tun da farko, babban jami’in WHO na shiyyar Arewa maso Yamma, a jihar Kano, Dakta Haruna Adamu, ya ce sun bayar da kayayyakin ne domin kara kaimi ga kokarin gwamnatin jihar Kano na karfafa matakan rigakafin kamuwa da cutar mashako a dukkan wuraren da abin ya shafa da kuma cibiyoyin kiwon lafiya.
Ya kuma yabawa jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf da ma’aikatar lafiya da sauran hukumomin gwamnati wajen shiga a dama da su don magance cutar da ta barke a jihar Kano.
Dakta Haruna ya ce, kayan ya kunshi katan 467 na kayan bayar da kariyar kai (PPEs) da sauran kayayyakin gwaje-gwaje don tallafa wa ayyukan dakile cutar a jihar Kano.
Abubuwan sun haɗa da rigunan kariya, jakar kariya daga haɗari, safar hannu ta gwaji (M, L, XL), safar hannu na tiyata (6.5, 7.5, 8.0, 8.5), da sauransu.