Connect with us

News

Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirinta na karfafa hukumar samar da magunguna (DMCSA) – cewar Kwamishinan Lafiya

Published

on

Spread the love

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

 

Domin tabbatar da dorewar isassun magunguna masu inganci da rahusa zuwa cibiyoyin kiwon lafiya na jihar, gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirinta na karfafa hukumar samar da magunguna (DMCSA) domin gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.

Advertisement

 

Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya yi wannan batun a lokacin da yake jawabi a wurin bude kwantaragin samar da magunguna na shekarar 2023/2024, wanda aka gudanar a harabar hukumar.

WHO ta bayar da gudummawar kayayyaki domin dakile cutar mashako a Jahar Kano

Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa kwanan nan DMCSA ta yi tallan kwantaragin samar da magunguna, inda aka gayyaci masu sha’awa kuma suka cancanta don samar da isassun da magunguna da sauran kayayyakin kiwon lafiya.

Advertisement

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in yada labarai na ma’aikatar lafiya ta jihar Ibrahim Abdullahi ya ce Dr. Labaran ya bayyana cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya bai wa fannin kiwon lafiya kulawa ta muhimmanci ta hanyar wanzar da kyawawan manufofi, ayyuka da tsare-tsare da nufin inganta lafiyar jama’ar jihar.

 

Kwamishinan ya ci gaba da cewa, rawar da DMCSA take takawa wajen samar da magunguna masu inganci da masu araha da kuma kayayyakin masarufi a wuraren jama’a ba karama ba ce, hakan ne ma ya sa gwamnatin Kano ke yin bakin kokarinta wajen tallafa wa hukumar a kowane lokaci don ta cimma manufofinta.

Advertisement

 

Ya ce gwamnati mai ci ta karbi ragamar hukumar ne da dimbin bashin masu samar da magunguna, ya ce hakan ne ya sa ma’aikatar lafiya a madadin gwamnatin jihar ta kira taro da masu samar da kayayyaki tare da ba su tabbacin hukumar na biyan dukkan basukan da suka kai kimanin Naira biliyan 1.2 na kwantaragin samar da magunguna da kuma samarwa ta gaggawa, inda ya yaba musu bisa fahimtarsu, goyon baya da hadin kai.

 

Advertisement

Dakta Labaran, wanda ya samu wakilcin Babbar Sakatariyar ma’aikatar, Hajiya Amina Aliyu Musa, ya yaba da jajircewar Gwamna Abba Kabir Yusuf da manufarsa ta kawo sauye-sauye masu inganci a duk tsarin kiwon lafiya na jihar.

 

Kwamishinan ya kara jaddada goyon bayansa ga hukumar wajen gudanar da bude bayar da kwantaragin da kuma tantance masu bukata, inda ya kuma ba da tabbacin cewa za a yi adalci da gaskiya wajen zabar wadanda suka samu nasara.

Advertisement

 

Tun da farko, Darakta Janar na DMSCA, Pharm. Gali Sule FPSN, ya tunatar da mahalarta taron cewa alhakinbhukumar ne samowa da kawo magunguna ga al’ummar jihar ta hanyar cibiyoyin kiwon lafiya mallakar jihar.

 

Advertisement

Ya kara da cewa, daga cikin ayyukan hukumar akwai samar da wadannan magunguna da wasu kayayyakin masu inganci, masu yawa kuma a farashi mai sauki ga jama’a, yana mai nuni dw cewa bude kasuwar wani kokari ne na cimma dukkanin manyan manufofin da aka samar da hukumar domin su.

 

Babban daraktan ya ce tsarin bayar da kwantaragin yana da matukar tasiri wajen siyan kayayyaki, inda masu bukata ke fafatawa da juna wajen samar da magunguna da sauran kayayyakin lafiya ga hukumar, inda ya jaddada cewa a karshen tsarin za a ba wa wadanda suka yi nasara damar samar da kayayyakin.

Advertisement

 

Pharm Gali ya ci gaba da cewa, tsarin kwantaragin, cikin farin ciki ya ce ya tabbatar wasu daga cikin masu samar da magunguna na bayar farashi mai sauki saboda sanin cewa mutane ne ke cin gajiyar kayayyakin, ba sayarwa ake don a ci riba ba.

 

Advertisement

Ya yaba wa masu samar da kayayyaki da suka shiga cikin shirin saboda farashin da suke bai wa gwamnati hakika wani bangare ne na bayar da gudummawarsu ga al’umma.

 

Damuwa da bashin makudan kudaden da shugabannin da suka gabata suka tara, DGn ya jinjina wa Kwamishinan bisa yadda ya shiga cikin lamarin a kan lokaci ta hanyar yin zama da masu kawo kayayyaki, inda aka tsara hanyoyin da za a bi wajen magance basussukan da aka gada na kusan Naira biliyan daya 1.2 daga shekarar 2019 zuwa 2023, inda aka tsara cewa cikin watanni 12 za a biya dukkan basussukan, kuma sun fara biya a watan jiya.

Advertisement

 

Da yake jawabi a madadin sauran masu bukatar kwantaragin, Auwalu Bala daga kamfanin JAWA International, ya yaba wa gwamnatin jihar Kano bisa tsananin damuwar da take da shi ga lafiyar al’ummar jihar, ya kuma yaba wa hukumar DMCSA bisa buda musu damar samar da magunguna don su nema.

 

Advertisement

Ya kuma ba da tabbacin duk wadanda suka samu nasara wajen samar da magunguna masu inganci domin biyan bukatun mutane na samun ingantattun magunguna, masu kyau da kuma araha a ko da yaushe.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *