News
Gwamnatin Kano Ta Daukaka Kara Kan Hukuncin Diyyar biliyan 30 saboda rusau a Filin Idi
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnatin Kano ta daukaka kara kan hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yanke na cewa ta biya diyyar Naira biliyan 30 ga wasu ‘yan kasuwar
Kotu ta bada diyyar Naira biliyan 30 ga ‘yan kasuwa, maimakon Naira biliyan 250 da suka nema daga gwamnati
Daukar matakin ya biyo bayan rusau da gwamnatin Kano ta yi tun farkon hawanta mulki.
Gwamnatin jihar Kano ta daukaka kara kan hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yanke na cewa ta biya diyyar Naira biliyan 30 ga wasu ‘yan kasuwar da ta rusawa shagunansu, Daily Post ta rawaito.
Kwamishinan lafiya na jahar kano ya kaddamar da allurar rukakafin cutar mashako
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano karkashin jagorancin mai shari’a Simon Anogede, a lokacin da ta ke yanke hukunci a shari’ar da kungiyar ‘yan kasuwa ta shigar, ta ce abin da gwamnati ta yi na zalunci ne da kuma saba wa kundin tsarin mulkin kasa.
Sai dai kotun ta bada diyyar Naira biliyan 30 ga ‘yan kasuwar, maimakon Naira biliyan 250 da suka nema daga gwamnati.
Alkalin ya bayar da umarnin a biya kudin nan take.
Sai dai gwamnatin jihar Kano ta ce ta daukaka kara kan hukuncin da ta bayyana a matsayin rashin adalci.
Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Barista Haruna Isa Dederi, ya bayyana cewa kotu ba ta yi daidai ba wajen yanke hukunci ga kungiyar ‘yan kasuwa saboda dokar amfani da filaye ta fito karara kan matsayin filaye a kowace jiha.
Ya dage kan cewa kotun ba ta da hurumin ko da sauraren karar saboda gwamnati ce kadai ta mallaki fili kamar yadda dokar amfani da filaye ta tanada.
