News
Kwamishinan lafiya na jahar kano ya kaddamar da allurar rukakafin cutar mashako
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Kwamishinan lafiya na jahira kano dr. Abubaka labaran Yusif ya kaddamar da rukakafin cutar mashako wanda tuni ansami bullar cutar a wasu kananan hukumumin jahar kano.
Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa Haka kuma ansami bullar wannan cutar ne a kasa da watani goma da suka gabata jahohi kano legas da wasu jahohi ashirin ciki har da Abuja.
Kotu ta ci tarar gwamnatin Jahar Kano biliyan 30 saboda rusau a Filin Idi
Kwamishinan lafiya yace Bayan anga bullar cutar kano sun bazama wajen ganin an tabbatar da ganin an magance wannan cutar
Wanda a dalilin haka aka samar da asibitoci guda biyu wajen magance cutar mashako a jahar kano
Sannan dukanin wanda suka kamu da wannan cuta ta mashako anabin yan uwa da masu jiya har gidaje ana basu rogakafin da magani wannan cutar.
Kawo yanzu jahar kano tasamu wanda suka kamu da wannan cutar mashako kimanin 9569 haka kuna 5300 sun sami lafiya ansallame su sunkoma gidajinsu
A wannan watane jihar kano ta samu rasa rayukan masu cutar kimanin 500 ,domin jihar kano ta tabbatar da wannan nasara da aka samu wajen magance wannan cuta damu da abokan aikin mins ma’aikatar lafiya ta tarayya da kuma ma’aikatar lafiya ta matakin farko da hukumar kula da cututuka masu ya duwa ta kasa NSDC sunyi tsarai tsare da zaishafi dukkanin al ummar jahir kano.
Daga karshe yayi kira ga al-umma gwammanti ta tsara za’ayi wannan ruga kafi daga gobe kuma ana saranaran za’ayi mutane muliyan daya da dubu dari wannan allurai, yana kira da mutane su fita sukai ya’yansu wannan allura a duganin guraran da aka kebe dan yin wannan allurai
Yakumace mutane sukarbi dukkanin rugakafi da akeyi irin su yanda,cutar sarke hakora, tarin duka,cutar fuliyo, ciwon hanta da saurain su ya kamata mutane su fita su karbesu
Ya kara kira ga al-umma har yanzu anacikin yanayin damuna wanda yanayine wanda yake jenyo cututuka irin su amai da gudawa,da san karau, al-umma ya kamata su kula da tsabyar mullin su dan a tabbatar da ankare kai daga wannan cututuka,
Inasu nayiamfani da wannan dama na godewa mai girma gwamman jihar kano Alhaji Abba kabir Yusif ,domin bawa al-ummar jihar kano kulawa da lafiyarsu ta musamman,ta yarda ya iya kwato asibiti Asiya bayaro da ingantashi da duba marasa lafiya kyauta da basu magani kyauta, a kalla mutane gubu daya a kullum sunazo suna karbar magani,
Daga karshe ya godewa abokan akinsa da yan jarida wajen tsananta bincike wajen wayarwa da al-umma kai game da wannan cuta
