News
Mutum 22 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Jahar Neja
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Mutum 22 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a ƙauyen Kasabu da ke jihar Neja.
Kwale-kwalen ya nitse ne da mutanen akan hanyarsa ta zuwa Kebbi.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya ruwaito darektan ba da agajin gaggawa na jihar ta Neja, Salihu Garba, na cewa masu ninƙaya na can suna ci gaba da aikin ceto.
Ya ce babu wani fasinja da aka ceto zuwa yanzu.
Ya alaƙanta hatsarin jirgin ruwan da cika da kogin ya yi.
Hatsarin ya afku ne a ranar Litinin lokacin da ake tsaka da cin kasuwar Yauri.
Wani labarin kuma Shari’ar gwamnan Kano: Hukumar DSS ta kama wata mata tana barazanar kai harin kunar bakin wake a Bidiyo
A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.
A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.
Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.
Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro