News
Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu Ya Bukaci Majalisa Ta Amince Masa Ya Ciwo Bashi
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya bukaci zauren majalisar dattawa ta kasa ta sahalle masa ciwo basusuukan kasashen waje domin gaggauta gudanar da wasu aiyukan raya kasa.
Hakan na zuwa ne a yayin da shugaban kasar ya nemi izinin majalisar wajen amincewa da kwarya-kwaryar kasafin kudin bana na naira tiriliyan 2 da milyan 176, domin aiwatar da Karin albashi na wucin gadi ga ma’aikata da kuma gudanar da aiyukan tsaro da sauran wasu aiyuka.
Kungiyar kwadago ta NLC Ta Zargi ‘Yansanda Da Lakadawa Shugabanta Duka.
A zaman zaurikan majalisun dokokin kasar na jiya sun yiwa kwarya-kwaryar kasafin kudin na bana karatu na biyu.
Bugu da kari shugaban kasar ta tura da daftarin tsare-tsaren kashe kudi na matsaikacin zango daga shekarar 2024 zuwa 2024 ga zaurikan majalisun domin samun amincewarsu.
A wani labarin kuma Kungiyar kwadago ta NLC Ta Zargi ‘Yansanda Da Lakadawa Shugabanta Duka.
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
