News
Tsohon gwamnan CBN, Emefiele ya koma gida bayan shafe kwanaki 151 a tsare
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
A jiya ne tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele, ya isa gidansa da ke Abuja, bayan da wata babbar kotun Abuja ta bayar da belinsa.
Ya shafe kwanaki 151 a hannun jami’an tsaro.
Rundunar Yan Sanda A Jihar Imo Sun Gargadi Masu Shirin Kawo Cikas Ga Zaben Gwamna Dake Tafe
Babbar kotun tarayyar da ke zamanta a Maitama ta bayar da umarnin a sake shi daga gidan yari, duk da rashin amincewar da babban lauyan gwamnatin tarayya, AGF, da hukumar yaki da cin-hanci da rashawa EFCC suka yi.
Kotun, a hukuncin da mai shari’a Olukayode Adeniyi ya yanke, ta bayar da umarnin a saki tsohon gwamnan babban bankin ga lauyoyinsa, duk da cewa ta umarce shi da ya miƙa dukkan takardun tafiye-tafiyen sa na kasashen waje.
A wani labarin kuma Rundunar Yan Sanda A Jihar Imo Sun Gargadi Masu Shirin Kawo Cikas Ga Zaben Gwamna Dake Tafe
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
