Connect with us

News

Sojojin Isra’ila da mayakan Hamas suna fafatawa a kan titunan Gaza

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD  ZAHRADDIN

 

Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare ta sama a Gaza a yayin da sojojin kasar suke bi layi-layi suna fafatawa da mambobin kungiyar Hamasa, sannan dubban Falasdinawa da ke nean mafaka suna ta tserewa zuwa kudancin Gaza.

Dubban Falasdinawa sun makale a yankin cikin “mawuyacin hali” a yayin da Isra’ila ta kwashe sama da wata daya tana kai musu hare-hare ta sama da kasa ba tare da samun isasshen abici da ruwa ba, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Tsohon gwamnan CBN, Emefiele ya koma gida bayan shafe kwanaki 151 a tsare

Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sha yin fatali da tayin tsagaita wuta yana mai cewa ba zai daina ba sai Hamas ta saki mutanen da ta yi garkuwa da su a Gaza.

A cewar wasu jam’iai, ana tattaunawa domin sakin mutum 12 da aka yi garkuwa da su, ciki har da Amurkawa shida, kafin a yarda a tsagaita wuta ta kwana uku.

Advertisement

A wani labarin kuma Tsohon gwamnan CBN, Emefiele ya koma gida bayan shafe kwanaki 151 a tsare

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending