Connect with us

News

Zaben Gwamnan Jahar Kogi: Jam’iyyun Siyasa Sun Amince Da Yarjejeniyar Zaman Lafiya 

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Gabanin zaben gwamnan jihar Kogi a ranar Asabar, jam’iyyun siyasa goma sha takwas da zasu fafata a zaben sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban kwamitin zaman lafiya na kasa, Janar Abdulsalam Abubakar mai ritaya, ya ja hankalin ‘yan takarar gwamna a jihar.

Sojojin Isra’ila da mayakan Hamas suna fafatawa a kan titunan Gaza

Abubakar, wanda John Onaiyekan ya wakilta, ya ce ya fara nuna shakku sosai a kan jajircewar ‘yan takarar da ke cikin irin wannan yarjejeniyar zaman lafiya wajen biyayya ga alkawarin.

Sai dai ya bukaci jam’iyyun da su tabbatar sun yi biyayya ga yarjejeniyar a lokacin zabe.

Advertisement

A wani labarin kuma Sojojin Isra’ila da mayakan Hamas suna fafatawa a kan titunan Gaza

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending