News
Hukumar Hisbah za ta sake gayyatar yan Kannywood a karo na biyu
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar Hisbah ta jihar Kano za ta sake gayyatar yan masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, cikin sigar gayyatar da suke buƙata ayi musu, bayan ƙin amsa kiran farko da mafi yawansu su kayi, bisa zargin cewa ba’a gayyace su bisa ƙa’ida ba.
Nassara Radio ta rawaito cewa Babban kwamandan hukumar, Sheikh Malam Aminu Ibrahim Daurawa, ne ya bayyana haka a ranar Talata yayin da ya karɓi bakuncin shugaban hukumar tace finafinai da dab’i ta jihar Kano, Abba El-Mustapha.
A wani labarin kuma Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
