Connect with us

News

Yajin aikin ƙungiyoyin ƙwadago haramtacce ne – Gwamnatin tarraya

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta bayyana rashin jin dadin ta game da matakin da kungiyoyin kwadago na kasa  NLC da TUC suka dauka na fara yajin aikin a fadin kasar, duk da umarnin da kotun ma’aikata ta bayar na kada su yi yajin aiki.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin ta bayyana matakin a matsayin wata alama ta girman kai da ƙoƙarin shafa wa gwamnati kashin kaji.

Advertisement

Daruruwan ‘ya’yan jam’iyyar PDP sun mamaye hedikwatar INEC da ke Yenagoa, suna neman a soke zaben Nembe.

Sanarwar wadda ta samu sa hannun mai taimaka wa shugaba Tinubu kan yaɗa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga ta ce “yajin aikin fatali ne da umarnin kotu da tozarta ɓangaren shari’a.”

 

Advertisement

Ta ƙara da cewa “Bai kamata ƙungiyoyin biyu su hukunta ƙasar baki daya ba kan wani lamari na ƙashin kai da ya shafi shugaban ƙwadagon, Joe Ajaero, wanda aka kai wa hari a Owerri”

 

Advertisement

Gwamnati ta jaddada kudirinta na gudanar da bincike kan harin da aka kai wa shugaban ƙungiyar Ajaero, inda ta ce babban sufeton ‘yan sanda ya bayar da umarnin a gudanar da bincike, kuma an canja kwamishinan ‘yan sandan jihar Imo.

 

Advertisement

Gwamnatin ta kuma jaddada cewa, yajin aikin, wanda ya bijirewa umarnin kotu, na nuni da rashin mutunta bangaren shari’a, kuma ya saɓawa ka’idojin kungiyar kwadago a tarihi.

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending