Connect with us

News

Gwamna Abba Kabir Yusuf Mai Kishin Harkar kiwon Lafiya ne – Kwamishinan Lafiya 

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

An bayyana kishin fannin lafiya da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke da shi a matsayin babban dalilin da ya sa aka samu ci gaba a fannin kiwon lafiya na jihar Kano gaba daya.

 

Advertisement

Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi a wajen wani taron bita na kwanaki 3 kan nazarin ka’idojin samar da kayan tazarar haihuwa na gwamnatin taya da za su dace da jihohi wanda ma’aikatar tare da hadin gwiwar kungiyoyin da ke tallafa wa lafiya suka shirya.

Yajin aikin ƙungiyoyin ƙwadago haramtacce ne – Gwamnatin tarraya

Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da Jami’in Yada Labarai na Ma’aikatar Lafiya ya turawa Jaridar Inda Ranka, inda ya ce an gudanar a jihar Kaduna.

Advertisement

 

Kwamishinan ya bayyana cewa, ana iya ganin muhimmancin kiwon lafiya a wajen Gwamnan a cikin jawabinsa na kasafin kudin shekarar 2024, inda aka ware sama da Naira biliyan 51 ga fannin don tabbatar da biyan bukatun jama’a kan kiwon lafiya da dukkan hukumomin lafiya na jihar.

Advertisement

 

Ya kuma tabbatar wa mahalarta taron cewa samun kudaden da za a yi wa jama’a hidima ba zai yi wahala a wannan gwamnati mai ci ba, domin Gwamna ya jajirce kan hakan a kowane lokaci, yana mai nuni da cewa abin da kawai ake bukata shi ne jajircewa da kuma jajircewar wadanda da ke aiwatar da shirye-shiryen.

Advertisement

 

Dakta Labaran, wanda Babban Daraktan Hukumar Kula da Cibiyoyin Lafiya Masu Zaman Kansu (PHIMA), Farfesa Salisu Ahmad Ibrahim ya wakilta, ya bayyana cewa Najeriya a matsayin ta tarayya, Kano tana da irin abubuwan da take da su daban da sauran jihohi, inda ya bukaci mahalarta taron da su yi nazarin ka’idojin sosai su ga yadda za su dace da bukatun al’ummar jihar Kano.

Advertisement

 

Dakta Labaran ya ce gwamnati mai ci ta yi nasarar kara kwarin gwiwa ga kamfanonin da ke samar da magunguna don su dawo da ayyukansu bayan sun gudu daga jihar saboda dimbin basussukan da ba a biya su ba, an tabbatar da cewa nan da shekara guda za a biya su baki daya.

Advertisement

 

Kwamishinan ya tabbar da cewa, daga cikin abubuwan da za a tattauna a cikin ka’idojin shi ne inda kamfanonin samar da magungunan za su iya shigowa, yana mai kara tabbatar da cewa hakan zai zama wata hanya inda gwamnati za ta shigo cikin sauki domin samar da magungunan yadda ya dace da zai kai lungu da sako na jihar.

Advertisement

 

A jawabinsa na maraba, Daraktan kula da Lafiyar Al’umma da Dakile Yaduwar Cututtuka, Dr. Ashiru Rajab ya tunatar da mahalarta tsron cewa a wasu shekarun baya an hana jahohi sayo kayayyakin tazarar haihuwa, inda ya kamata su rika karbar kayayyakin kyauta domin rabawa da kuma amfani da su kyauta a asibitoci.

Advertisement

 

Ya bayyana cewa, akwai wani asusu a matakin kasa da gwamnatin tarayya da sauran abokan hulda sukan sanya kudi, inda ya koka da cewa saboda tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan asusun ba aikin da ya kamata ya yi.

Advertisement

 

Dakta Rajab ya ci gaba da cewa, duba da yadda lamarin ya faru, sai akayanke shawarar a bar jihohi su sayi kayayyakin tazarar haihuwa da kansu amma bisa taka tsantsan, wato ba yadda suka ga dama ba.

Advertisement

 

Ya bukaci mahalarta taron da su bi ka’idojin cikin gida da su duba abin da aka sanya a cikin kundin su tsara shi ta yadda zai amfani al’ummar jihar Kano.

Advertisement

 

Da take bayyana manufofin gudanar da taron, Jami’ar kula da Lafiyar Haihuwa da Tazarar Haihuwa ta jiha, Dakta Umma Abubakar Isah, ta ce an shirya shi ne da nufin fayyace ma’auni da tsarin kididdiga; da sanin yadda za a samu daidaito da tsarin samar da kayan tazarar haihuwa na ƙasa da kuma gano yadda tsarin yake domin gujewa tsari mai rikitarwa.

Advertisement

 

Sauran, in ji ta, su ne killace tsari mafi dacewa don tabbatar da sayen ingantattun kayayyakin tazarar haihuwa; ayyana tsarin bayar da rahoton kayayyakin da aka saya a matakin ƙasa da jihohi; gano taimakon da ake buƙata daga UNFPA, USAID da sauran abokan haɗin gwiwa; da kuma ayyana rawar da jihohi da ma’aikatar lafiya ta tarayya za su taka wajen sa ido da tantance yadda ake aiwatar da ka’idojin.

Advertisement

 

Kungiyoyi masu zaman kansu da ke tallafawa fannin lafiya irin su Bill and Melinda Gates Foundation, Lafiya Project, A360, Options, iDevPro, YPE4H, da dai sauransu sun nuna goyon baya ga aikin nazarin ka’idojin da za a yi, tare da baya da gudummawa mai muhimmanci don tabbatar da shi mai ƙarfi wanda zai aiwatu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending