Connect with us

News

Wani Mutum Ya Rataye Kansa A Jihar Kano

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

An tsinci gawar wani mutum mai suna Saleh Abdullahi mai shekaru 35 a duniya bayan ya rataye kansa a wani daki da ke unguwar Sharada a Kano.

An ce wanda aka kashe ya bar rubutacciyar takarda da ta fara da: “a yi hakuri.” Amma sauran ba a iya karanta su ba

Advertisement

Ɗan majalisar Kasar Amurka ya yi wa takwaransa gula

Daily Trust ta rawaito cewa sun samu labarin cewa an ce yana zaune ne a gidan dan uwansa, Idris Hamisu l.

 

Advertisement

Hamisu ya shaida cewa, “Na dawo daga sallar asuba, matata ta so yi wa ‘ya’yanmu abinci, kuma tana neman ashana domin ta kunna wuta amma babu.

Ta tuna Salisu yakan yi amfani da turaren gida. Da ta aiko yaronmu ya karbo ashana, sai yaron ya gan shi a rataye, sai ya koma da gudu yana ihu wai wani ne ya rataye Yaya Saleh. Sai na garzaya daki na ga gaskiya ne”.

Advertisement

Da aka tambaye shi ko yana da wata matsala shi marigayin, sai ya ce, “Ba mu sami wata matsala ba. Abin da na sani shi ne cewa a kwanakin nan ya damu, kuma a matsayinmu na ’yan kasuwa, muna jin haka idan kasuwa ta lalace.

‘’Mu ’yan kasuwa ne kuma muna cinikin kayan daki, amma Saleh wani lokaci ya kan sayo da sayar da tsofaffin kayan.

Advertisement

“Ya nuna alamun damuwa a kwanakin nan saboda ya karbi kudi a hannun wani ya siyo kayan da kudinsu ya kai N400,000 a Rijiyar Zaki daga hannun wasu mutane suka kai shi gidan inda suka ajiye kayan suka ce ya dawo wata rana ya kai su.

Da ya nemi lambar wayarsu, sai suka ce tunda ya ga gidan zai iya dawowa kowane lokaci, kuma da ya koma daga baya bai samu gidan ba.

Advertisement

Abin da ya jawo masa damuwa kenan domin kudin ba nasa ba ne kuma mai shi ya matsa masa ya biya shi.”

 

Advertisement

Babu wani martani daga rundunar ‘yan sandan kan lamarin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending