News
Masu Garkuwa Da Mutane 4 Sun Shiga Hannu A Jihar Jigawa
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa ta cafke wasu mutum hudu da take zargi da ta’adar garkuwa da mutane a Karamar Hukumar Ringim.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu Adam, ya ce ‘yan sandan sun kuma kama wani mutum mai kera bindigogi.
Ya ce sun kwato bindigogi kirar gida guda uku, shanu 29, tumaki hudu, sarka daya da kuma babur kirar Boxer guda daya.
Aminiya ta ruwaito cewa DSP Adam ya bayyana cewa, a ranar 16 ga watan Nuwamba, 2023, ‘yan sandan da ke aiki a sashen Ringim karkashin jagorancin Baturen ‘yan sandan yankin tare da hadin gwiwar ‘yan banga, suka kama mutumin mai shekara 50 da ke zaune a kauyen Yandutse Kawari, a Karamar Hukumar Ringim, wanda ya kware wajen kera bindigogi.
A wani labarin kuma Kungiyar ASUU Ta Koka Kan Karancin Malamai A Jami’oi
Ministan harkokin wajen ƙasar China, Wang Yi, zai je birnin New York domin karbar baƙuncin taron Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a karshen wannan mako, yayin da ƙasashen duniya ke ci gaba da ƙokarin shiga tsakani a rikicin Isra’ila da Hamas.
Gabanin taron, Jordan ta sake sabunta kiran a mayar da yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta ta wucin gadi ta zama dindindin.
Yayin da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya sake nanata muhimmancin da Isra’ila ke da shi na daukar “matakan hakika” don rage cutar da fararen hula a Gaza.
