News
Godwin Emefiele Zai Yi Bukin Kiristimeti Da Sabuwar Shekara A Gidan Gyaran Hali
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Tsohon gwamnan babban bankin kasa CBN, Godwin Emefiele, zai yi bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara a gidan gyaran hali na Kuje.
Hakan ya faru ne saboda kasa cika sharuddan bada belinsa da ya yi a ranar Talata. Bayan zaman kotun a jiya jami’an hukumar gidan gyaran halin sun sake tafiya da Emefiele.
Kotun Daukaka Kara da ta kori Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC Na zargin Emefiele da aikata lefuka guda shida da suka hada da saba yarjejeniyar bada kwangila ga wani kanfanin zuba jari, da kuma yin almundahanar kudi.
A wani labarin kuma Kotun Daukaka Kara da ta kori Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa
Gwamnatin Taliban a Afghanistan ta ce mai taimaka wa firaministan ƙasar kan tattalin arziƙi, Abdul Ghani Baradar, ya ƙaddamar da rijiyoyin haƙar man fetur takwas a yankin arewacin ƙasar.
A lokacin bikin ƙaddamarwar, Ghani ya ce za a gina makeken asibiti da madatsar ruwa da kuma kwalta a yankin haƙar man fetur ɗin na Amu Darya.
Bayanin da gwamnati ta fitar ya ce ƙaddamar da rijiyoyinn zai ƙara yawan ɗanyen man fetur da Afghanistan ke haƙowa a kowace rana zuwa cubic mita 800 a kowace rana, yayin da nan gaba ake sa ran ƙaddamar da wasu ƙarin rijiyoyin guda 10.
Yanzu haka dai injiniyoyi 350 da sauran ma’aikata 550 ne ke aiki a filin haƙar ɗanyen man fetur ɗin na Amu Darya.
A kwanakin nan ne Afghanistan ta fara aikin neman rijiyoyin ɗanyen mai a arewacin Afghanistan tare da haɗin gwiwar wani kamfanin ƙasar China mai suna ‘Afchin’.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
