Sports
An dage karawar da Bayern Munich za ta yi da Union Berlin saboda dusar kankara a babban birnin Munich
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
An dage karawar da Bayern Munich za ta yi da Union Berlin saboda dusar kankara a babban birnin Munich kamar yadda hukumomi suka tabbatar a ranar Asabar.
An shirya gudanar da wasan ne a ranar Asabar da yamma amma sanarwar manema labarai daga Bayern ta ce hatsarin tsaro da yanayin zirga-zirga ya sanya aka dage wasan.
Gwamnan Kano ya kaddamar da fara biyan ƴan fansho sama da mutune 5,000 haƙƙunan su
Karancin yanayin zafi ya haifar da dusar kankara a kudancin Jamus, musamman a Munich.
Gabanin soke wasan dai tuni hukumomin sufuri na birnin Munich suka dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a yankin mafi girma na Munich, yayin da cunkoson ababen hawa suka tsaya cak.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, Bayern ta ce akwai hatsari mara misaltuwa ga ‘yan kallo kuma ta bayyana cewa akwai wahalar isa filin wasa na Arena.
Hukumar kula da kwallon kafa ta Jamus (DFL) da ke gudanar da gasar Bundesliga ta tabbatar da soke gasar a ranar Asabar kuma ta ce nan ba da jimawa ba za a sanar da sabuwar ranar da za a buga wasan.
-
News6 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
