Connect with us

News

Za a shiga mummunar yanayi a Gaza idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba – MDD

Published

on

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya (MDD), Antonio Guterres

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya (MDD), Antonio Guterres, ya aika da wasiƙa ga kwamitin tsaro na majalisar, inda ya nemi ƴan kwamitin su yi gaggawar ɗaukar mataki domin kauce wa ɓarkewar mummunar annoba a Gaza.

Advertisement

“Yayin da ake fuskantar rashin isar agajin gaggawa a Gaza, ina jawo hankalin Kwamatin tsaron domin a gaggauta yin wani abu domin kauce wa afkawa cikin mummunar yanayi sannan da yin kira da a gaggauta tsagaita wuta don a samu damar kai agaji Gaza,” in ji Guterres a cikin wani saƙo da ya wallafa ranar Laraba.

Hukumar Shari’a Ta Dakatar Da Alkali Kan Yanke Hukunci Ta Hanyar Da Ba Ta Dace Ba

Cikin wasiƙar da ya rubuta, Guterres ya nanata cewa yanayin na ƙara ƙazancewa cikin sauri, ta yadda ba za a iya gyara wa Falasɗinawa komai ba daga baya da kuma tsaron yankin.

Advertisement

Ya ƙara jaddada buƙatar tsagaita wuta saboda yadda lamarin ke ƙara ƙazancewa a Gaza, da kuma dawo da neman zaman lafiya a yankin.

Guterres yace “Wannan ne karon farko da nake fitowa ƙarara in yi irin wannan kira ga kwamitin majalisar domin halin da ake ciki yanzu ya ƙazanta a Gaza matuƙa tun bayan zama na sakatare janar na MDD a 2017”.

Advertisement

Bugu da kari, Guterres ya ce alhakin ƙasashen duniya ne su shiga tsakani domin kawo ƙarshen yaƙin.

Ya yi amfani da sashen doka ta 99 ta MDD, wadda ta ba shi damar yin irin wannan kira da jawo hankalin Kwamatin Tsaro kan “duk wani batu da yake ganin zai iya barazana ga zaman tsaro da zaman lafiya na kasashen duniya.”

Advertisement

A yayin da ake ci gaba da kai hare-haren, Mista Guterres ya ce lamarin idan ya ci gaba ba a tsaida shi ba zai iya kara tsananta barazanar da ake fuskanta na wanzar da zaman lafiya da tsaron kasa da kasa.”

Ya yi gargadin cewa zaman lafiyar jama’a a Gaza na iya wargaje nan ba da jimawa ba a daidai lokacin da tsarin ayyukan jin kai ke durkushewa.

Advertisement

“Halin da ake ciki yana kara tabarbarewa da zai iya haifar da matsaloli ga falasdinawa gaba daya da kuma zaman lafiya da tsaro a yankin.”

“Ina tsammanin zaman lafiyar jama’a zai wargaje nan ba da jimawa ba saboda hali mai tsanani da ake ciki, wanda hakan zai sa ko da karancin taimakon jin kai ba zai yiwu ba,” in ji shi.

Advertisement

Haka kuma, ya yi nuni da cewa, sama da mutane 1,200 a Isra’ila ‘yan ta’addar Hamas suka kashe su a ranar 7 ga Oktoba, ciki har da yara 33, da kuma mutane 130 da har yanzu ake tsare da su.

“Dole ne a sake su ba tare da wani sharadi ba. Batun cin zarafin jima’i a lokacin wadannan hare-haren yana da ban tsoro,” in ji shi.

Advertisement

Ya jaddada cewa idan aka tsagaita wuta, akwai fatan zaman lafiya da kuma damar kai agajin taimako.

Amma duk da haka, jakadan Isra’ila na Majalisar Dinkin Duniya, Gilad Erdan bai amince da kiran da Mista Guterres ya yi kan mataki na sashen doka ta 99 ta MDD ba.

Advertisement

 

Premium Times 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending