Connect with us

News

Sanusi Lamido Ya Bukaci Shugaba Tinubu Ya Sauka Daga Mukaminsa Ministan Man Fetur 

Published

on

Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Mallam Muhammadu Sanusi na II

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Mallam Muhammadu Sanusi na II, ya shawarci shugaban kasa Bola Tinubu da kada ya rike ofishin ministan albarkatun man fetur.

Da yake jawabi a wajen taron shugabannin bankunan da aka gudanar ranar Alhamis a Abuja, Sanusi ya ce irin wannan tsari zai sa kasar nan ta shiga wahala wajen rike kamfanin man fetur na Najeriya.

Advertisement

Za a shiga mummunar yanayi a Gaza idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba – MDD

Sanusi wanda shi ne gwamnan babban bankin kasa daga watan Yunin 2009 zuwa Fabrairu 2014, ya caccaki kamfanin NNPC Limited da gazawa wajen tura isassun kudaden waje a cikin asusun gwamnati duk da cire tallafin man fetur.

Ya jaddada bukatar daidaita kasuwar musayar kudaden waje, inda ya ce manufofin hada-hadar kudi a cikin shekaru takwas da suka gabata sun haifar da hauhawar farashin kayayyaki da koma bayan tattalin arziki a kasarnan.

Advertisement

Shima, wani dattijon kasa kuma tsohon ministan kudi, Cif Olu Falae, ya ce ba sai shugaban Najeriya ya zama ministan man fetur ba, yana goyon bayan matsayar tsohon gwamnan CBN, Muhammadu Sanusi.

Falae ya kuma yi amanna cewa, nada ministan man fetur zai sa a samu wanda za a tuhuma a lokacin da al’amura suka tabarbare.

Advertisement

Idan za’a iya tunawa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rike mukamin ministan mai a lokacin da yake kan Mulki inda shima a Bola Tinubu yabi Irin tsarin.

Amma dattijon ya ce ya kamata ma’aikatar man fetur ta samu minista ba shugaban kasa ba.

Advertisement

A wani labarin kuma Za a shiga mummunar yanayi a Gaza idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba – MDD

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Advertisement

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Advertisement

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending