Connect with us

News

Da hannun wasu ‘manyan ƙasa’ cikin ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda a Nijeriya -Minista

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Ministan Ma’adinai, Mr Dele Alake, ya bayyana cewa da hannun wasu manyan ƙasa a harkar ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda da haƙar ma’adinai ta ɓarauniyar hanya a Nijeriya.

Jaridar  Blueprint ta rawaito cewar, Alake ya yi wannan tonon sililin ne sa’ilin da ya bayyana a gaban Kwamitin Majalisar Wakilai Kan Ma’adinai don kare kasafin ma’aikatarsa na shekarar 2024 a Abuja.

Advertisement

An kashe ‘yan Najeriya sama da dubu 5 tun bayan darewar Tinubu kan mulki

Kazalika, Ministan ya yi zargin akwai baƙi da ke haƙar ma’adinai a Nijeriya ba bisa ƙa’ida ba.

Don haka ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta maida hankali sosai kan fannin ma’adinai wanda ka iya samar wa ƙasa biliyoyin Naira duk shekara.

Advertisement

Sama da shekara 13 ‘yan ta’adda na addabar shiyoyin Arewa maso Yamma, Arewa maso Gabas, tsakiyar Nijeriya da sauran sassan ƙasar.

‘Yan ta’addan sun yi ƙarfin da a wasu lokutan sukan kai hari su mamaye ƙauyuka inda suka nemi kuɗin fansa bayan sun yi garkuwa da mutane. Wasu lokutan kuma sukan ƙona gidajen jama’a bayan sun kwashi dukiya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending