Connect with us

News

Kwai Alƙalai, Ƴan Majalisa da manyan jami’an gwamnati dake ɗirka sata – ICPC

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Hukumar ICPC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a jami’an gwamnati, ta bayyana munmunar shaidar cewa ɓangaren shari’a, ‘yan majalisa da manyan jami’an gwamnati cike suke da masu cin rashawa da satar maƙudan kuɗaɗe.

Premium Times ta ruwaito cewa Shugaban Cibiiyar Yaƙi da Cin Rashawa, Tunde Babawole ne ya bayyana haka, wurin Taron Tantance Geji da Malejin Rashawa da Cin Hanci a Najeriya, wanda aka gudanar a Abuja.

Yan bindiga sun saki ɗaliban jami’ar Dutsinma bayan shafe fiye da wata biyu a tsare

Babawale ya ci gaba da cewa bincike ya gano cewa cin hanci da rashawa a ɓangaren majalisa, kotuna da manyan jami’an gwamnatin tarayya, har ma da ɓangaren harkokin masu zaman kan su, ya kai kashi 42 bisa 100 a 2022 da 2023.

“An bankaɗo cewa dukkan ɓangarorin uku cike suke danƙam da masu aikata rashin gaskiya ta hanyar wawurar kuɗaɗe, cin hanci da rashawa.

“Sai dai kuma duk da a jihohi ma lamarin ya yi muni, amma kuma ba duka aka zama ɗaya ba. Saboda wasu jihohi ba su kai wasu jihohin munin rashawa da satar kuɗaɗe ba.

Advertisement

“Amma da muka yi masu kuɗin goro, sai muka haƙƙaƙe cewa munin matsalar ya kai gejin kashi 42 bisa 100.”

Ya ce cin hanci, rashawa da satar kuɗaɗe sun yi yawa da muni a Najeriya, har ta kai ga akwai buƙatar gagarimin aikin wayar wa mutane da kai, cusa masu ɗa’a da sauya masu tunani zuwa kishin ƙasa ba kashe ƙasa ba.

“Saboda zuciyoyin mutane sun ƙeƙashe, kwata-kwata ba su yi wa harƙalar satar kuɗaɗe kallon wani abin kunya.

“Ya kamata mu horas da matasa har ma da manyan magidanta, mu cusa masu kishin ƙasa da kyawawan ɗabiu da kuma ƙyamar cin rashawa,” inji shi.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending