News
Kayan Masarufi Sun Sake Tashin Gwauron Zabi A Nijeriya -NBS
DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
Hukumar Kididdiga Ta Kasa (NBS), ta ce farashin kayayyaki sun kara hauhawa, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, kuma rabon da a ga hakan tun a shekarar 1996.
Nijeriya dai na fuskantar hauhawar farashin kayan masarufi da sauran nau’ikan kayayyakin amfanin yau da kullum.
Shugaban Hukumar kula Da Asibitocin Jihar Kano Ya Dakatar Wasu Ma aikata
A rahoton da ta fitar NBS, ta ce an samu karin hauhawar farashin kayayyaki a watan Nuwamba da kashi 0.87 cikin 100, idan aka kwatanta da watan Oktoban da ya gabata.
Hauhawar farashin kaya a Nijeriya yanzu ya haura kashi 27.33 cikin 100 zuwa kashi 28.20 ciki 100, kuma rabon da a shiga irin wannan yanayi na tashin farashin kayayyaki tun 1996.
Kazalika, hukumar ta ce wannan mataki na hauhawar farashin kaya ya karu da kashi 6.73 cikin 100, idan aka kwatanta da watan Nuwamban shekarar 2022, wanda ya ke a matakin kashi 21.47 cikin 100.
Rahoton, ya ce hauhawar farashin kayayyaki na watan Nuwamba ya wuce adadin da aka kiyasta a watan Oktoban da ya wuce.
Leadership ta ruwaito cewa hauhawar farashin kayan abinci ya karu da kaso 32.84 cikin 100 a shekarar 2023, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata wanda yake a matakin kaso 24.13 cikin 100.
Rahoton, ya kara da cewa kayayyakin da suka ta’azzara hauhawar farashin sun hada da farashin Burodi, man girki, doya da kuma dankalin turawa, sauran kayan kuwa su ne kifi, nama da saura kayan kwalam da makulashe da kuma na shayi.
‘Yan Nijeriya dai na zuba idon ganin abin da gwamnati za ta fito da shi domin kawo karshen yadda farashi kayayyaki ya ke tashi.
A wani labarin kuma Shugaban Hukumar kula Da Asibitocin Jihar Kano Ya Dakatar Wasu Ma aikata
Yanzu dai Babu wani Abu da al’ummar jihar kano ke yawan tattaunawa akansa Kamar batun shari’ar zaben gwamnan jihar.
Wakilin jaridar Inda Ranka Yasir Sani Abdullahi ya gano yadda kusan da yawa daga cikin wuraren zaman alumma da kasuwanni harma da ofisoshin gwamnatin da masu zaman Kansu, Babu wani batu da yafi daukar hankali Kamar batun shari’ar
Magoya bayan dukkan babgarorin manyan jam’iyyun APC Dana NNPP na bugar kirgin samun nasara a kotun koli.
Jam’iyyar APC na da kwarin guiwar cewa Zata Kara samun nasara a kotun koli kasancewar kotun farko da ta biyu duka ta Bata nasara
Sai dai jam’iyyar NNPP Bayan korafe korafe da tayi akan hukunce hukunce na kotun baya, yanzu ta bayyana kwarin guiwar da take dashi na samun nasara a kotun koli.
Al’ummar jihar kano da dukkan bangarorin manyan jam’iyyun APC Da NNPP na dakon hukuncin na karshe na kotun koli wadda ake saran Zata yanke cikin karshen watan Nan, shi zai kawo karshen jayayya da kowane bangare keyi a jihar kano.
Masu iya magana na cewa Shari’a mace ce da ciki ba’asan wa Zata Haifa ba.
