Connect with us

News

An Kama Ma’auratan Da Suka Sayi Jaririn Wata Daya A Kan 30,000

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Rundunar ‘yansandan Jihar Anambra ta yi nasarar cafke wasu ma’aurata da ke da hannu wajen safarar wani jariri dan wata daya.

Rahotanni sun bayyana cewa ma’auratan sun sayi jaririn ne a hannun mahaifiyarsa da ke unguwar Ajah a jihar Legas kan kudi kadan kan kudi naira 30,000.

Advertisement

Yadda ‘Yan Kauyen Mutunji Na Jihar Zamfara Suka Mutu Saboda Yunwa A Hannun ‘Yan Bindiga

Har yanzu dai ba a bayyana sunayen ma’auratan ba, amma jami’an ‘yansanda sun cafke su a Onitsha lokacin da suke kokarin shiga wata mota da jaririn a ranar Lahadi.

 

Advertisement

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yansandan Anambra, DSP Ikenga Tochukwu, ya bayyana cewa ‘yansandan sun yi gaggawar ceto jaririn tare da mika shi ga ma’aikatar harkokin mata da kananan yara ta jihar.

 

Advertisement

 

Tochukwu ya ci gaba da cewa, an mika ma’auratan ga hukumar hana fataucin mutane ta kasa (NAPTIP) ta jihar domin ci gaba da bincike.

Advertisement

A cewarsa an gano su a lokacin da wani fasinja da ke cikin motar ya sanar da ‘yansanda yana zargin cewa ma’auratan na dauke da jaririn da ba nasu ba.

Leadership ta ruwaito cewa Ya bayyana cewa mai ba da labarin ya sanar da ‘yansanda cewa ya lura cewa a lokacin da suke tafiya daga Legas, jaririn na kuka, amma matar ta gaza ba shi nono.

Advertisement

Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Aderemi Adeoye, ya yaba wa mutumin kan taimaka wajen ceto yaron.

Ya kuma yaba da kwazo da taka-tsan-tsan da jami’an ‘yansanda suka yi wajen magance lamarin cikin gaggawa.

Advertisement

A wani labarin kuma Yadda ‘Yan Kauyen Mutunji Na Jihar Zamfara Suka Mutu Saboda Yunwa A Hannun ‘Yan Bindiga

Yanzu dai Babu wani Abu da al’ummar jihar kano ke yawan tattaunawa akansa Kamar batun shari’ar zaben gwamnan jihar.

Advertisement

Wakilin jaridar Inda Ranka Yasir Sani Abdullahi ya gano yadda kusan da yawa daga cikin wuraren zaman alumma da kasuwanni harma da ofisoshin gwamnatin da masu zaman Kansu, Babu wani batu da yafi daukar hankali Kamar batun shari’ar

Magoya bayan dukkan babgarorin manyan jam’iyyun APC Dana NNPP na bugar kirgin samun nasara a kotun koli.

Advertisement

Jam’iyyar APC na da kwarin guiwar cewa Zata Kara samun nasara a kotun koli kasancewar kotun farko da ta biyu duka ta Bata nasara

Sai dai jam’iyyar NNPP Bayan korafe korafe da tayi akan hukunce hukunce na kotun baya, yanzu ta bayyana kwarin guiwar da take dashi na samun nasara a kotun koli.

Advertisement

Al’ummar jihar kano da dukkan bangarorin manyan jam’iyyun APC Da NNPP na dakon hukuncin na karshe na kotun koli wadda ake saran Zata yanke cikin karshen watan Nan, shi zai kawo karshen jayayya da kowane bangare keyi a jihar kano.

Masu iya magana na cewa Shari’a mace ce da ciki ba’asan wa Zata Haifa ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending