News
Yadda ‘Yan Kauyen Mutunji Na Jihar Zamfara Suka Mutu Saboda Yunwa A Hannun ‘Yan Bindiga
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kwanaki ashirin da biyar bayan sace wasu mutanen kauye 150 a gundumar Mutunji dake karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara, uku daga cikin wadanda al’amarin ya shafa sun mutu saboda yunwa yayin da ‘yan fashin daji suka yi shiru kan batun kudin fansar sauran Mutane 147.
Idan ba a manta ba Arewa Radio ta rawaito a ranar Juma’a, 24 ga watan Nuwamba na 2023 ‘yan bindigar suka kai hari kauyuka shida a gundumar Mutunji inda suka yi awon gaba da mutane 150 saboda gazawar su na biyan harajin Naira miliyan 200 da shugaban ‘yan bindigar Damina ya dora musu.
Sai dai wani mazaunin garin ya shaida wa jaridar dailytrust cewa mutane ukun da aka ruwaito sun mutu ta yiwu sun mutu ne saboda yunwa, yana mai cewa ’yan kungiyar da suka yi garkuwa da su suna karkashin jagorancin wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga ne, Damina, wanda ya shahara wajen cin zarafin wadanda suka yi garkuwa da su.
Mazauna garin ya ce jama’a sun koma yin addu’o’in neman taimakon Allah domin kawo karshen ayyukan ta’addanci a yankin.
Rundunar ‘yan sanda ba ta ce komai ba kan al’amarin a kwanakin nan.
A wani labarin kuma Kotu Ta Haramta Wa Tsohuwar Minista Rike Mukami A Nijeriya
Yanzu dai Babu wani Abu da al’ummar jihar kano ke yawan tattaunawa akansa Kamar batun shari’ar zaben gwamnan jihar.
Wakilin jaridar Inda Ranka Yasir Sani Abdullahi ya gano yadda kusan da yawa daga cikin wuraren zaman alumma da kasuwanni harma da ofisoshin gwamnatin da masu zaman Kansu, Babu wani batu da yafi daukar hankali Kamar batun shari’ar
Magoya bayan dukkan babgarorin manyan jam’iyyun APC Dana NNPP na bugar kirgin samun nasara a kotun koli.
Jam’iyyar APC na da kwarin guiwar cewa Zata Kara samun nasara a kotun koli kasancewar kotun farko da ta biyu duka ta Bata nasara
Sai dai jam’iyyar NNPP Bayan korafe korafe da tayi akan hukunce hukunce na kotun baya, yanzu ta bayyana kwarin guiwar da take dashi na samun nasara a kotun koli.
Al’ummar jihar kano da dukkan bangarorin manyan jam’iyyun APC Da NNPP na dakon hukuncin na karshe na kotun koli wadda ake saran Zata yanke cikin karshen watan Nan, shi zai kawo karshen jayayya da kowane bangare keyi a jihar kano.
Masu iya magana na cewa Shari’a mace ce da ciki ba’asan wa Zata Haifa ba.
