News
Kotu Ta Haramta Wa Tsohuwar Minista Rike Mukami A Nijeriya
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Babbar Kotun Tarayya da ke birnin tarayya, Abuja ta haramta wa tsohuwar Ministar Mata da Walwalar Al’umma, Pauline Tallen sake rike wani mukamin gwamnati.
A wani hukunci da ta yanke a ranar Litinin, kotun ta yi tir da kalaman da tsohuwar ministar da ta yi a shekarar da ta wuce, inda ta caccaki wani hukuncin kotun tarayya da ke Jihar Adamawa.
Zaben Adamawa: Hudu Ari Ya Yanke Jiki Gabanin Gurfanar Da Shi A Gaban Kotu
Kotun da ke zamanta a birnin Yola, babban birnin Adamawa, ta soke cancantar takarar A’ishatu Dahiru Binani ta jam’iyyar APC da ke neman kujerar gwamnan jihar.
Sai dai Tallen ta nuna rashin gamsuwarta da hukuncin na kotun wanda ta bayyana a matsayin “musgunawa wani bangare na al’umma”, yayin da ta bukaci ‘yan Nijeriya da su yi watsi da hukuncin.
Leadership ta ruwaito cewa Shugaban lauyoyi na kasa, Yakubu Maikyau ya bukaci Tallen da ta nemi afuwa kan kalamanta, inda har ya yi barazanar maka ta a gaban kuliya.
Sai dai tsohuwar ministar ba ta nuna halin ko-in-kula ba, abin da ya sa kungiyar lauyoyin ta maka ta a gaban kotu.
A wani labarin kuma Zaben Adamawa: Hudu Ari Ya Yanke Jiki Gabanin Gurfanar Da Shi A Gaban Kotu
Yanzu dai Babu wani Abu da al’ummar jihar kano ke yawan tattaunawa akansa Kamar batun shari’ar zaben gwamnan jihar.
Wakilin jaridar Inda Ranka Yasir Sani Abdullahi ya gano yadda kusan da yawa daga cikin wuraren zaman alumma da kasuwanni harma da ofisoshin gwamnatin da masu zaman Kansu, Babu wani batu da yafi daukar hankali Kamar batun shari’ar
Magoya bayan dukkan babgarorin manyan jam’iyyun APC Dana NNPP na bugar kirgin samun nasara a kotun koli.
Jam’iyyar APC na da kwarin guiwar cewa Zata Kara samun nasara a kotun koli kasancewar kotun farko da ta biyu duka ta Bata nasara
Sai dai jam’iyyar NNPP Bayan korafe korafe da tayi akan hukunce hukunce na kotun baya, yanzu ta bayyana kwarin guiwar da take dashi na samun nasara a kotun koli.
Al’ummar jihar kano da dukkan bangarorin manyan jam’iyyun APC Da NNPP na dakon hukuncin na karshe na kotun koli wadda ake saran Zata yanke cikin karshen watan Nan, shi zai kawo karshen jayayya da kowane bangare keyi a jihar kano.
Masu iya magana na cewa Shari’a mace ce da ciki ba’asan wa Zata Haifa ba.
