Connect with us

Politics

Zaben Cike Gurbi: APC Za Ta Sayar Da Takardar Tsayawa Takarar Sanata Naira Miliyan 20

Published

on

APC 4

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Gabanin zaben ‘yan majalisar dokokin tarayya da na jiha da za a yi a ranar 3 ga watan Fabrairu, jam’iyyar APC ta ayyana Naira Miliyan 20 kudin na gani inaso na tsayawa takarar sanata.

Haka kuma jam’iyyar ta ayyana Naira miliyan 10 kan neman takarar tsayawa dan majalisar wakilai ta tarayya sannan kuma za a biya Naira miliyan biyu ga duk mai sha’awan tsayawa takarar kujerar majalisar dokokin jiha.

Advertisement

Sakataren jam’iyyar APC na kasa, Sulaiman Argungu, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Litinin, ya yi bayani dalla-dalla cewa, takardar neman takarar kujerar Sanata Naira miliyan 3 ne, sannan takardar tsayawa takara Naira miliyan 17 – jimilla ya kama Naira Miliyan 20.

Kungiyar SERAP Ta Maka Kamfanin Man Fetur Na Kasa NNPCL A Kotu

Argungu ya kuma ce takardar neman takarar kujerar majalisar wakilai ya kai naira miliyan daya sannan takardar tsayawa takara Naira miliyan 9 yayin da ‘yan majalisar jiha za su biya Naira N500,000 da Naira Miliyan N1.5 na nema da tsayawa takara.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending