News
Harin Yan Bindiga Da Ya Faru A Filato Babban Abin Tashin Hankali Ne -Shehu Sani
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Tsohon Sanata mai wakiltar jahar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Nijeriya Sanata Shehu Sani ya mayar da martani kan wasu munanan abubuwan da suka faru a jihar Filato a jajibirin Kirsimeti.
Yan bindiga dai sun kai hare-hare a lokaci guda kan al’umma sama da goma sha biyar a kananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi na jihar a jajibirin Kirsimeti.
Kungiyar Manyan Likitocin Dabbobi Tayi Allah Wadai Da Kashe Wasu Kananan Giwaye Da Aka Yi A Borno
‘Yan ta’addan sun kona gidaje daban-daban a daren Lahadi, sannan sun yi awon gaba da kayan gona tare da lalata dukiyoyi yayin da suke yanka mutanen.
Daily Post ta ruwaito cewa Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, a ranar Talata, ya bayyana a gidan talabijin na Channels Television’s Sunrise Daily cewa adadin wadanda suka mutu a harin jajibirin Kirsimeti a jihar ya haura 115.
Sai dai da yake magana kan lamarin, Sani, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Talata, ya ce ya kalli bidiyon sakamakon kisan gillar da aka yi a Filato, inda ya kara da cewa inda wani jariri ke kuka a bayan gawar mahaifiyarsa ne yafi tayar da hankali.
Ya kuma bayyana wannan lamari mai cike da bakin ciki a matsayin daya daga cikin munanan ayyukan ta’addancin da ya taba gani.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News3 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
