Connect with us

News

An Kama Wani Ɗan Shekara 17 Da Laifin Damfarar Mai Pos N900,000 A Jihar  Jigawa

Published

on

DAGA MUHAMMAD BASHIR MUSA

 

Advertisement

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke wani yaro dan shekara 17 mai suna Abdulmuminu Tasiu bisa laifin damfarar wani mai siyar da POS kudi naira 900,000 a karamar hukumar Maigatari.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da turawa da Jaridar DAILY POST.

Advertisement

Hukumar EFCC ta sake bude babin binciken wasu tsofaffin gwamnoni 13

A cewar sanarwar, “Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a inda wani mai suna Aminu Mustafa mai shekaru 38 a unguwar Unguwar Dodo da ke karamar hukumar Maigatari mai siyar POS ya baiwa wani abokin ciniki injin din ya shigar da lambar sirrinsa domin ya ciro kudi.

“Mai sana’ar POS din ya kai rahoto ga ‘yan sanda cewa wani da ba a san ko wanene ba ya zo shagon sa na POS ya ciro kudi wanda bayan ya ba shi na’urar POS ya yi amfani da ita Wajen damfarar sa  sannan ya tura kudi naira dubu dari tara (N900,000.00k) a asusun sa.

Advertisement

“Da samun bayanan, an sanar da ‘yan sandan da ke sintiri; An yi sa’a, an kama Abdulmuminu Tasi’u dan shekara 17 mai suna Adakawa quarters, karamar hukumar Dala Kano, aka kawo shi ofishin domin bincike.”

Shiisu ya ce da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amince da aikata laifin.

Advertisement

Ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu bayan an gudanar da bincike

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending