Connect with us

News

Zamu cigaba da baiwa gwamna goyon baya domin ayyukan cigaban Kano: Dan majalisa mai wakiltar Bebeji Hon. Ali Muhd Tiga.

Published

on

DAGA AMINU ABDULLAHI 

Dan majalisar dokokin Kano mai wakiltar Bebeji Hon. Ali Muhd Tiga ya taya Abba Kabir Yusuf, murnar nasarar da ya samu a kotun koli.

Advertisement

Cikin sanarwar da ya fitar shugaban kwamitin kasuwanci a majalisar dokokin Kano, ya ce bayyana nasarar Abba Kabir Yusuf da kotun koli tayi nasara ce ga al’ummar Kano baki daya.

Ɓangaren shari’ar Najeriya ya fara farfaɗo da kimarsa – Masana

Ya kuma godewa alkalan da suka jagoranci hukuncin wajen tabbatar da gaskiya, yana mai cewa hakan ya karawa bangaren kima a idon al’ummar kasar nan.

Advertisement

Ya ce lokaci ne da alummar jihar Kano zasu cigaba da yiwa gwamna Abba Kabir Yusif addu’a domin cigaba da bijiro da ayyukan cigaba.

Ali Muhd Tiga, ya kara da cewa a matsayin sa na shugaban kwamitin kasuwanci a zauren majalisar dokokin Kano zai maida hankali wajen kawo kudiri da shirye-shirye na bunkasa kasuwanci a Kano.

Advertisement

Ya kuma ce majalisar zata cigaba da baiwa gwamna Abba Kabir Yusif goyan baya domin gudanar da ayyukan cigaba a jihar nan.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending