Connect with us

News

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta Ciyar da Ma’aikatanta Gaba

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

 

A kokarinta na kara kaimi da kwarin gwiwar ma’aikatanta don ci gaba da gudanar da ayyukansu da kyau, Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta yi wa ma’aikatanta karin girma.

Da yake jawabi a lokacin gudanar da intabiyu ga ma’aikatan, Shugaban Kwamitin Ciyar da Ma’aikatan Gaba wanda kuma shi ne Darakta Gudanarwa na Ma’aikatar, Shehu Sani Shehu, ya yi kira ga ma’aikatan da za a kara wa girma da su ribanya kokari wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na gudanar da ayyuka mai inganci.

Akalla shaguna 100 ne suka kone a wata gobarar da ta tashi a Kasuwar Panteka da Kaduna.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da Jami’in Yada Labarai na Ma’aikatar Lafiya Ibrahim Abdullahi ya tura wa Jaridar Inda Ranka.

 

Advertisement

Daraktan ya tunatar da su cewa gwamnati mai ci ta Alhaji Abba Kabir Yusuf ta ba da kulawa ta musamman ga walwalarasu ta hanyar ciyar da su gaba a kan lokaci, inda ya bukace su da su rama alheri da alheri ta hanyar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, yana mai tsoratarwa da cewa ma’aikatar ba za ta amince da sakaci da rashin zuwa aiki daga kowane ma’aikaci ba.

 

Shehu Sani ya bayyana cewa karin girma ya kasance na watannin Janairu da Yuli ne na shekarar 2023, inda manyan ma’aikata 40 da kananan ma’aikata 14 za a yi wa intabiyu, a ba su maki sannan a daga likkafarsu bayan sun amsa tambayoyi daga mambobin kwamitin karin girman, ya kara da cewa haka kuma kwamitin zai tattauna bukatar wasu ma’aikatan na koma wa wasu guraben aikin.

 

Daraktan ya bukace su da su kasance masu karfin zuciya, su guji firgita tare da amsa tambayoyin gwargwadon iliminsu, inda ya ba su tabbacin cewa tambayoyin suna da sauki, kai tsaye suke ba kwana-kwana, kumaa cikin bangarorin da suka kware.

 

Advertisement

Ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa hazakarsa wajen samar da kyakkyawan salon shugabanci abin sha’awa da ke shafar rayuwar al’ummar Kano, ya kuma yaba masa bisa irin kulawar da yake bai wa tsarin kiwon lafiya da ba a taba ganin irinsa ba a jihar.

 

Shehu Sani ya kuma yaba wa Dakta Abubakar Labaran Yusuf bisa samar da dukkan abubuwan ake bukata na gudanar da shirin ciyar da ma’aikatan gaba cikin nasara wanda hakan ke nuni da cewa Kwamishinan ya damu matuka da kuma sanya jin dadin ma’aikatansa a cikin zuciyarsa.

 

Ga mambobin kwamitin, Daraktan ya bukace su da su kasance masu juriya wajen yi ma’aikatan da za a kara wa girma tambayoyi cikin sauki da sakin fuska domin su sa musu nutsuwa da karfin gwiwa wajen amsa tambayoyin yadda ya kamata.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending