Ɗan wasan Super Eagles Sadiq Umar, a karon farko ya fito ya yi bayani dangane da ce-ce-ku-ce da ake yi kan cire shi daga ƙungiyar Super Eagles bayan buga wasan farko, sai kuma surutan da suka biyo bayan ganin sa da aka yi ya buga wa ƙungiyar sa ta Spain wasa, wato Real Sociedad, kwanaki biyar bayan bayanna cewa ya ji rauni.
A bayanin da ya yi a shafin sa na Instagram, Umar ya bayyana wa ‘yan Najeriya cewa ya samu ɗan rauni ne a wasan Najeriya da Guinea, inda ‘yan bayan Guinea biyu suka mauje shi ya faɗi, har Najeriya ta samu bugun fanereti kuma ta ci ƙwallo, aka tashi 1-1.
An Zabi Mace Ta Farko A Matsayin Shugabar Karamar Hukuma A Jihar Borno
Ya ce washegari duk da ciwon da ya ji, ya ci gaba da wasa har aka tashi, alhali an ce a cire shi ɗin, sai ya ce zai iya ci gaba.
To washegari sai guiwar Umar ta ɗan kumbura, dalilin da tilas sai likitoci sun duba shi kenan.
“Likitocin Super Eagles sun duba ni washegari, suka ce ƙoƙon guiwa ta ya gurɗe. Daga nan sai kociya ya maye gurbi na da wani ɗan wasan, bayan likitoci sun ba shi shawarar yin hakan. Ni kuma aka cire ni daga Gasar AFCON.”
Premium Times ta ruwaito cewa Daga nan sai suka tura Umar Spain, domin ta lafiya ya yi jiyyar makonni uku.
“Yayin da na isa kulob ɗi na, sai likitocin can suka sake yi min wani sabon gwaji. Daga nan suka ce ai ƙoƙon guiwa ta bai gurɗe ba, ‘yar buguwa ce dai kawai sai wani ɗan ƙwarzane. Daga nan suka ce na jijjiga ƙafa ta na koma tirenin kawai.
Umar ya bar Abidjan ya koma Spain ranar 12 ga Janairu, sai aka gan shi ya na tirenin a ranar 15 ga Janairu. Ranar 17 ga Janairu kuma sai ga shi ya buga wasan sa kulob ɗin sa ya yi nasa kan Osasuna a Gasar Copa Del Rey. An saƙa Umar a minti na 73.
An yi ta mamakin yadda Super Eagles ta maida shi Spain, domin idan dai da gaske gurɗe guiwa ya yi, to ba zai iya yin wasa a cikin sati ɗaya ba.
Jama’a da dama na cewa an dai cire shi ne don a maye gurbin sa da Iheanacho kawai.
