Connect with us

News

An kama Shugaban Karamar Hukuma kan zargin yunkurin kisan Kakakin Majalisa

Published

on

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO 

 

Advertisement

Rundunar ƴan sandan Nijeriya ta ce ta yi nasarar kama wasu mutum biyu, ciki har da wani Shugaban Ƙaramar Hukumar Jihar Binuwai da ake zargin su da hannu a yunƙurin kashe Kakakin Majalisar Dokokin jihar.

“Daga cikin waɗanda aka kama ɗin har da wani Shugaban ɗaya daga cikin Ƙanana Hukumomin Jihar Binuwai,” kamar yadda sanarwar rundunar ƴan sandan ta ƙasa mai ɗauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a ACP Olumuyiwa Adejobi, ta faɗa.

Advertisement

Yan bindiga sun kutsa Tashar Nagulle sun gudu da mutum 31, a yankin Batsari

Sanarwar ta ƙara da cewa binciken farko ya bayyana cewa ana zargin Shugaban Ƙaramar Hukumar da haɗa baki da wani ɓata gari da nufin ya kashe Kakakin Majalisar Dokokin Jihar ta Binuwai, Hon. Aondona Hycenth Dajoh.

Ba tare da ɓata lokaci ba sai jami’an sashen Leƙen Asiri da Tawagar Gaggawa ta Leƙen Asiri suka yi abin da ya dace bayan samun bayanan sirri a kan shirin yunƙurin kisan kan.”

Advertisement

Rundunar ƴan sandan ta ce a yanzu haka waɗanda ake zargin suna hannunta, kuma suna bayar da haɗin kan da ya dace wajen gudanar da binciken da ake yi.

 

Advertisement

Ƴan sanda sun kuma tabbatar da cewa waɗanda ake zargin sun fuskanci hukunci shari’a idan har aka tabbatar da laifinsu.

 

Advertisement

Kazalika rundunar ta nanata wa ƴan Nijeriya cewa ba za ta yi ƙsa a gwiwa ba wajen ba su kariya da kuma tabbatar da bin doka da oda a kowane mataki.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending