News
Jami’ar ADUSTECH ta dakatar da malamin da ya saka dalibai tsallen kwado
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar Jami’ar kimiyya da fasaha dake Kano ta Aliko Dangote University of Science and Technology Wudil, KUST Wudil ta dakatar da malamin Jami’ar, Dr. Barbushe bayan wani bidiyo ya yaɗu na malamin ya saka wasu ɗalibai tsallen kwaɗo da daga hannu a sama wato “Kneel down” saboda ana zargin sun yi latti ne ko surutu a aji lokacinda yake lakca.
Rahotanni na nuni da cewa lamarin dai ya jawo surutu da ƙorafe-ƙorafe daga ko ina wasu na goyon bayansa wasu na sukarsa.
Cikin masu adawa da wannan tsarin ladaftarwa har da wani fitaccen Lauya a Kano, Barrista Abba Hikima wanda ya kira abun da cewa cin zarafin daliban ne kuma ya nemi hukumar jami’ar su hukunta lakcaran
A wata sanarwa da ta fitar yau Talata dauke da sa hannun mataimakin babban jami’in makarantar, Saidu Abdullahi Nayaya, ya ce an dakatar da malamin kuma an gurfanar dashi a gaban kwamitin ladaftarwa na Jami’ar
Hukumar Jami’ar ta kuma baiwa iyaye da dalibai haƙuri kan abunda malamin yayi.
ME MUTANE KE CEWA?
Wani dalibin a makarantar mai suna Hamza Muhammad Tilde cewa “Dr. Barbushe Allah ya kareka daga sharrin mutane. Wallahi wannan malamin mutumin kirki ne kuma jajir cewar sa a harkan koyar wa ba’a magana. Komai yakeyi burinsa kawai ayi dariya ne sabida yan aji su fahimta. Kayi tunani, malamin da yake daukan almost all faculties na KUST Wudil kuma kowa bayaso ya missing lectures nasa. So wannan hoton ba abun da za’ayi amfani dashi bane domin kaluba lentarsa domin ba’a san menene silar yin hakan ba, watakil ma misali akeyi domin yana koyar da “ASPECT OF MORALITY” kaga watakil duk a cikin koyar wane. We love you Barbushe” -Hamza Muhammad Tilde
Yaron Oga kuma ya ce “Munyi Allah wadai da sanya Ƙwamarawa Ɗaga hannu da tsallan ƙwaɗo a jami’ar KUST WUDIL, Wannan cin zarafin Ɗan adam da ƙwamaranci ne, ba za mu lamunci wannan ba.
Jamia akwai hanyoyi na ladaftar da dalibi bata hanyar chin zarafi nashi ba
Wannan malami baka keutata ba koda wasa kake high school ba secondary bace” -Musty Yaron Oga
Abdallah Tilde kuma ya ce “Nikam wannan lecturer ya burge ni!
Wannan lecturer Uba ne, Zaka samu yanada yara da kuma jikoki, don haka yasan irin radadin da iyaye sukeji a duk lokacin da akace yaransu sun Fadi jarabawa ko Kuma an basu suspension.
A irin wannan lokaci na tsadan kudin makaranta yayi dai dai, Saboda jami’a ba iya karatu ake koya ba, harda dabi’u ma. Ni Jami’ar da nayi karatu ma Motor nasu shine LEARNING AND CHARACTER.. Allah ya karama wannan Professor nisan kwana. Duk lokacin danaje KUST Zan ziyarce shi Insha Allah.” – Abdallah Tilde
