News
Kwamitin Inganta Sashin Sarrafa Magunguna Da Na Hade DRF Din KSCHMA Da Asibiti Sun Gabatar Da Rahotonsu
DAGA NUASIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Kwamitin inganta sashin sarrafa magunguna (DMU) na Hukumar Samar da Magunguna ta jiha (DMCSA) da na hade DRF na KSCHMA da na asibiti sun gabatar da rahotonsu.
Jaridar Inda Ranka ta ruwaito cewa Kwamishinan Lafiya, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, a ranar 21 ga Nuwamba, 2023, ya kaddamar da kwamitocin biyu tare da ba da sharuddan yin aiki a kai don samun nasarar aiwatar da ayyuka tare.
Jami’ar ADUSTECH ta dakatar da malamin da ya saka dalibai tsallen kwado
Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da jami’in yada labarai na Ma’aikatar Lafiya Ibrahim Abdullahi ya turawa da Jaridar Inda Ranka.
Sanarwar ta kara da cewa taron da ya gudana a dakin taro na DMCSA, Dakta Labaran ya bayyana cewa, hukumar ta DMCSA na da alhakin samar da magunguna masu inganci da rahusa ga cibiyoyin kiwon lafiya na jihar, wadanda ba za a iya yin su ba sai ta sashin sarrafa magunguna na Hukumar da ke samar da su a cikin gida domin rage radadin da talakawa ke fuskanta.
Kwamishinan ya tabbatar da cewa inganta sashin na DMU ya dace kuma ya zama wajibi domin a halin yanzu manufofin da ake amfani da su kan magunguna a kasar nan sun koma ga samar da magunguna a cikin gida, wanda gwamnatin tarayya za ta ware kudade don haka.
Ya bukaci mahukuntan DMCSA da su yi amfani da wannan damar su nemo hanyar da za su samu wadannan kudaden, yana mai jaddada cewa, idan aka samu kudaden, za a iya amfani da su wajen gaggauta inganta sashin na m DMU domin ya yi aiki yadda ya kamata don tabbatar da samar da magunguna masu inganci da rahusa kana ba tare da tsagaitawa ba kamar yadda mutane ke fata.
Dangane da hade DRF na KSCHMA da na asibiti kuwa, Dr. Labaran ya bayyana cewa an lura cewa kusan dukkanin asibitoci suna yin abin da suke so ne game da tsarin KSCHMA, duk da cewa an samu ci gaba a halin yanzu musamman saboda duba su akai-akai da ake yi.
Kwamishinan ya jaddada shawarar da kwamitin ya bayar na daidaita ayyukan KSCHMA da asibitoci a duk asibitocin da ake aiwatar da tsarin DRF da KSCHMA da za a yi bi da bi, ya kara da cewa hakan ya dace domin bai wa kwamitin damar horar da masu ruwa da tsaki daga asibitoci a kan dabarun hadewar.
Ya godewa mambobin kwamitin bisa jajircewarsu wajen ganin sun kammala ayyukan a kan lokaci, yana mai ba su tabbacin cewa za a yi nazari sosai kan rahotannin tare da duba shawarwarin da suka bayar domin karfafa ayyukan hukumomin biyu.
Tun da farko a nasa jawabin, Babban Daraktan Hukumar Samar da Magunguna (DMCSA) Pharm. Gali Sule ya bayyana cewa samar da magunguna masu inganci ga al’ummar Kano na daga cikin alkawuran da Mai Girma Gwamna ya yi tun a lokacin yakin neman zabe, kuma shi ne babban dalilin da ya sa Kwamishinan ya ga wajabcin inganta sashin sarrafa magunguna domin ya gudanar da aiki yadda ya kamata.
Ya ce sashin yana aiki ba kawai a matsayin samar da magunguna ba har ma a matsayin cibiyar horarwa saboda jami’o’i masu yawa suna tura dalibansu na SIWES don a horar da su a sashin, don haka bai kamata a bar shi yana aiki kasa da matsayinsa ba.
A nata bangaren, Sakatariyar Zartarwar ta KSCHMA, Dakta Rahila Muhktar, ta yaba da namijin kokarin Alhaji Abba Kabir Yusuf na ba da dukkan kulawar da ake bukata a sashin kiwon lafiya na jihar, sannan ta kuma yaba da irin jajircewar da Dakta Labaran ke da ita tare da kasancewa a shirye a ko da yaushe don ganin an inganta fannin.
Ta tabbatar da sadaukarwar hukumarta na tabbatar da ingantattun ayyukan KSCHMA masu inganci a asibitoci domin biyan bukatun abokan hulda.
