Connect with us

News

Wata Gobara ta Hallaka Wani Yaro Dan Shekara 4 a Kano

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wani yaro mai kimanin shekaru hudu mai suna Abubakar Sani sakamakon gobarar da ta tashi a Yakasai Layin Inuwa mai mai karamar hukumar birnin kano .

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi ya bayyana hakan a Kano.

Advertisement

An Kama ’Yan Najeriya 9 A Farfelan Jirgin Ruwa Za Su Je Turai

Saminu ya bayyana cewa, hukumar ta samu kiran gaggawa daga ma’aikacinsu Habibi Adamu game da barkewar gobara a Yakasai.

Ya kuma yi nuni da cewa, nan take aka hada tawagar ceto daga Ofishin hukumar kashe gobara dake Sakatariyar Audu Bako a birnin Kano .

Advertisement

Jami’in hulda da jama’a ya yi nuni da cewa, ginin bene daya mai tsawon mita 40 da 30 da ake amfani da shi a matsayin gidan zama, daki daya dake benen ne ya kone gaba daya sakamakon gobarar, yayin da falo daya ya dan kone.

Ya ce, Yaron ya makale a dakin da wuta ta kama har ta cinye shi kuma duk kokarin da aka yi na ceto shi kafin isowar ‘yan kwana-kwana ya ci tura.

Advertisement

Saminu ya ci gaba da cewa, an ceto wanda abin ya shafa a sume kuma aka kai shi asibitin kwararru na Murtala Muhammed, inda likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da rasuwarsa.

Jami’in hulda da jama’a ya bayyana cewa, an mika mamacin ga mahaifinsa, Sani Hussaini domin yi masa jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Advertisement

Ya ce gobarar ta tashi ne sakamakon yadda yaron da abin ya shafa ke wasa da ashana a cikin daki.

Saminu ya bukaci iyaye da su daina jefa ’ya’yansu cikin hadari ta hanyar barin su ba tare da kula da su ba da kuma nisantasu da abubuwa masu hadari .

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending