Connect with us

News

Yan bindigar da suka sace mata 53 da ke rakiyar kai wata amarya sun saki wani bidiyo da ke nuna matan tsaye cikin daji.

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

‘Yan bindigar da suka sace mata 53 da ke rakiyar kai wata amarya a jihar Katsina a makon da ya gabata, sun saki wani bidiyo da ke nuna matan tsaye cikin daji.

Advertisement

A ranar Alhamis da daddare ne ‘yan bindigar suka yi garkuwa da matan masu rakiyar amarya har da direban motar da suke ciki a karamar hukumar Sabuwa da ke jihar ta Katsina.

Tsadar Rayuwa: Majalisar Wakilai Ta Nemi Gwamnatin Tarayya Ta Lalubo Mafita

Abin da bidiyon ‘yan bindigar ya kunsa

Advertisement

A bidiyon mai tsawon minti 2:20, an ga dan bindiga sanye da kayan sojoji dauke da bindiga. Sun nuna matan sanye da hijabi a tsaye cikin surkukin daji. Cikin matan, akwai guda biyu masu rike da jariri.

Bidiyon ya nuna amaryar sanye da kakin soji da bindiga a wuyanta sai wani mutum wanda bisa jawaban ‘yan bindigar ke nuna shi ne direban motar da wata mata dukkansu rataye da bindiga a wuya.

Advertisement

“In kuma akwai wanda zai iya amsar su dai ya jarraba ya gani.” Wadan nan sune kalaman da aka fara ji cikin bidiyon da ‘yan bindigar suka saki a ranar Talata.

Kalaman ‘yan bindigar dai na nuna yanayi na kalubalantar duk wani mai iko da zai iya kubutar da matan da kuma direbansu da suka sace.

Advertisement

An kuma jiyo wani dan bindiga daga gefe yana Fulatanci yayin da guda a cikin su ke fassara kalmominsa da Hausa.

Sun kuma yi ikirarin mata 63 ne suka yi garkuwa da su ba 53 da gwamnatin Najeriya ta sanar an sace. Sai dai mai maganar da farko ya ambata 53 kafin daga bisani wata murya ta gyara masa zuwa 63.

Advertisement

‘Yan bindigar sun yi barazanar daura wa amaryar aure idan har ba a biya kudin fansa ba.

Bayan sun gama wadannan bayanan ne kuma aka nuna matan suna rokon hukuma ta kai musu agaji cikin shasshekar kuka.

Advertisement

“A taimaka mana, hukuma ba za ta kwace mu ba, a kawo kudi don Allah, ba a yi mana wulakanci ba.” in ji matan da aka nuna a bidiyon.

Ba duka ba zagi, ba abin da aka yi mana amma muna neman taimako, a taimaka mana, “don Allah ku taimaka mana, ” – kalaman da matan suka yi ta fada ke nan.

Advertisement

Daga baya kuma, ‘yan bindigar sun bukaci shi ma direban motar ya matso gaba ya yi bayani inda aka ji yana cewa jama’a su kai musu dauki saboda gwamnati ba za ta iya ba.

A cewarsa, “a taimaka mana, a taimaka mana, ‘yan uwanmu su kawo kudi a fanshe mu, a sallame mu, gwamnati ba za ta iya wannan aiki ba, ya fi karfinta wannan aikin, an kawo mu ba duka ba zagi, Alhamdulillahi,” in ji mutumin da aka ayyana direban ‘yan rakiyar amaryar ne.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending