Connect with us

News

Tsohon Ɗan Majalisa Ya Mutu Yayin Kallon Wasan Najeriya Da Afrika Ta Kudu

Published

on

Tsohon ɗan Majalisar Tarayyar, Cairo Ojougboh ya mutu sakamakon bugun zuciya yayin kallon wasan Najeriya da Afrika ta Kudu.

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO

 

Advertisement

Tsohon ɗan Majalisar Tarayya daga jihar Delta, Cairo Ojougboh ya mutu sakamakon bugun zuciya yayin kallon wasan Najeriya da Afrika ta Kudu.

Cairo Ojougboh ya yanke jiki ya mutu ne a daidai lokacin da za a yi bugun daga kai sai mai tsaron rago a wasan hamayya a gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON).

Advertisement

Marigayin ya kasance dan jam’iyyar APC ne kuma mai yawan babatu a kan batutuwan da suka taso a zauren majalisa.

Rahotanni na nuni da cewa wasan Najeriya da Afrika ta Kudu, wanda a karshe Najeriya ta yi nasara, ya yi zafi sosai, kuma ya tayar da kura a soshiyal midiya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending