Connect with us

News

Duk Wanda Ya Rike Al-Qur’ani, Ba Zai Taba Tozarta Ba, Ba Zai Wulakanta Ba, Kuma Ba zai Tsiyace Ba  —Malam Jafar

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Hakika babu wata babbar ni’ima da Allah ya yiwa wannan al’ummah bayan ni’imar aiko da Annabi Muhammad (SAW) kamar bamu Alqur’ani mai girma. Mu rike Alqur’ani domin riko da shi alkhairi ne duniya da lahira.

Advertisement

Mai Unguwar Bachirawa titin jajira Malam Abdulkadir Adamu na wannan jawabi ne yayin bikin saukar alqur,ani mai girma da makarantar Sheikh Harun littahfizul qur,an wa ulumihi, ta gudanar karo na 25 na dalibai 7 Mata Hudu Maza Uku.

Aliko Dangote ya yi alkawarin tallafa wa Kano a fannin lafiya da taimakon marasa galihu

Wanda 2 daga cikin daliban Maza sukayi sauka ta 3, yayin da Mace Daya daga cikin Ukun tayi sauka ta 2, sai kuma Sauran dalibai Masu sauka dai,dai. Saukar dai ta Gudana ne a Unguwar Bachirawa titin jajira bayan gidan mai Badosa, dake karamar Hukumar Ungoggo, inda yace hakkin yaya akan iyayensu shine sanya su a makarantun addini da na zamni domin sauke hakkin ne zai sanya su hadu da ubangiji salin.

Advertisement

Shima a nasa jawabin Shugaban Makarantar Sheikh Harun littahfizul qur,an wa ulumihi, Shekh malm Ja,afar Haruna Ja,afar dutsen wai, jan hankalin daliban yayi da su mai da hankulansu kan da su rungumi karatun alkur,ani mai girma domin samun nasara a cikin al,amuran yau da kullum na rayuwa.

 

Advertisement

Wakilin jaridar Inda Ranka da ya kasance a gurin Kabiru basiru fulatan ya rawaito cewa Saukar dai ta samu halartar manyan baki na ciki da wajen Unguwar ciki harda Babban Limamin Unguwar Malam Muhammad Salisu da akafi sani da Malam Imamu Rijiyar Lemo.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending