News
Za A Bude Shafin Baiwa Daliban Nigeria Rancen Kudi A Ranar 21 Ga Watan Fabrairu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Jaridar TheCable ta ruwaito cewa shugaban Bola Ahmed Tinubu zai kaddamar da shirin bayar da lamuni na dalibai da ake jira a hukumance a Abuja ranar 21 ga watan Fabrairu.
Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa lamunin yana buɗe ne ga duk ɗaliban Najeriya a manyan makarantun ƙasar, tare da tsarin biyan kuɗi mai sauƙi wanda zai fara daga shekaru biyu na samun aikin hidimar ƙasa.
Zan Fasa Rumbunan Kayan Abinci Da Aka Ɓoye A Kano – Muhyi Rimin Gado
Tinubu ya kuma ba da umarnin a saka ’yan Najeriya da suka cancanta da ke da ilimin boko da kuma wadanda ke jami’o’i masu zaman kansu a cikin shirin.
Daliban da a halin yanzu suka shiga jami’o’i ne kawai za a ba su kashi na farko na shirin kamar yanda Jaridar TheCable ta ruwaito.
Mr. Akintunde Sawyerr, sakataren zartarwa na Asusun ba da lamuni na ilimi na Najeriya (NELFUND), ya tabbatar wa TheCable ranar kaddamar da shirin.
Dangane da ka’idojin zaɓe, mai nema dole ne ya zama ɗan Najeriya kuma dole ne ya kasance ɗalibi na gaskiya a manyan makarantun ilimi a Najeriya.
A dandalin abubuwan da TheCable ta fahimci za a bayyana a yayin kaddamar da shirin, za a bukaci masu nema da su samar da muhimman bayanan sirri kamar lambar (NIN),da kuna (BVN) da lambar JAMB
An sanar da TheCable cewa za a bayar da lamunin ne kai tsaye ga makarantun ta hanyar asusun ajiyar kudi na NELFUND da ke babban bankin Najeriya (CBN) ba tare da wani mai shiga tsakani ba.
kwamitin na musamman na NELFUND nan ba da jimawa ba.
Membobin kamar yadda doka ta tanada, sune: gwamnan babban bankin kasa CBN a matsayin shugaba; babban sakataren NELFUND a matsayin sakatare; wakilin ministan ilimi; da kuma shugaban hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC).
Sauran su ne: wakilin dandalin mataimakan shugabannin jami’o’in Najeriya; Wakilin taron shugabanni na dukkan makarantun kimiyya da fasaha na Najeriya na dukkan kwalejojin ilimi a Najeriya; wakilin ministan kudi, babban mai binciken kudi na tarayya; wakilin kungiyar kwadago ta Najeriya NLC; wakilin kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA); da kuma wakilin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU).
Majalisar Dokoki ta kasa ta amince da dokar lamunin Dalibai (Access to Higher Education) a shekarar 2023 don samar da sauki ga ‘yan Najeriya masu karamin karfi ta hanyar lamuni mara ruwa, kuma Tinubu ne ya sanya wa hannu a ranar 13 ga Yuni, 2023.