News
Tsadar Rayuwa: Sarkin Kano Yayi Kira Ga Gwamnatin Tarayya Data Duba Halinda Al’umar Najeriya Suke Ciki
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayaro yayi kira ga Gwamnatin Tarayya data duba halinda Al’umar
Najeriya suke ciki na tsananin kunci kan hauhawar kayan abinci da rashin zaman lafiya a arewacin Kasar.
Sarkin yayi wannan kira ne a lokacin da Uwar gidan shugaban kasar Nigeria Senator Remi Tuninbu data ziyarceshi a fadarsa.a yau
Alhaji Aminu Ado Bayero ya kara da cewa Senator Remi tayi kokari wajan fadada aikinta na alheri da takeyi a jahar kano subada yawan Al umar da jihar kano take dasu.
Datake nata jawabin Uwar gidan Shugan kasar ta bayyanawa sarkin cewa tazo jihar kano ne domin tagodewa Al umar kano bisa goyan bayan da suka bawa mijinta alokacin zabe.
Daga karshe tayi alkawarin isar da sakon al’umar Kano da Arewacin Nigeria ga mai gidannata.bola tinubu
Uwar gidan shugaban kasar Senator Remi Tinubu tasamu rakiyar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa na kasa Senator Barau Jibrin da Gwamnan jihar Benue da matar shugaban majalisar wakilai na kasa da Uwar gidan Gwamnan Kano.
Tsadar Rayuwa: Sarkin Kano Yayi Kira Ga Gwamnatin Tarayya Data Duba Halinda Al’umar Nigeria Suke Ciki