News
Kungiyar Masu Saida Sarka da Dan Kunne Ta Kasuwar Sabon Gari Ta Gudanar da Sahihin zaben Shugabancin Kungiyar
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kungiyar masu saida sarka da dan kunne wacce akafi sani da Jewelry Dealers Development Association wato (JEDDA) dake kasuwar Sabon Gari sun gudanar da zaben jagororin kungiyar
Jaridar Inda Ranka ta ruwaito cewa an gudunar da zaben ne a GSS Stadium kusa da Kano Pillars Stadium kan titin zuwa filin jirgi.
Rahotanni na nuni da cewa masu neman jagorancin kungiyar sun hada da yan takarar chairman, mataimakin chairman, magatakarda, ma’aji, mai kyautata Jin dadin al’umma, da dai sauran su
Zaben ya gudana ne a ranar asabar inda mabiya wannan kungiya suka fito kwansu da kwarkwata suka bada hadin kai a wajan.
Saidai a Ziyarar da Sarkin Kasuwar Sabon Gari Alhaji Nuhu indabo yakai wajen zaben, ya bayyana Jin dadin sa yadda ‘yaga ‘yan kungiyar masu saida yari suka gudanar da zaben cikin koshin lafiya ba tare da samun rikiciba
Indabo ya Kara da cewa duk wanda ya sami wanan nasarar cin zaben dama wanda bai ci ba duk daman can abu daya ne ya hadasu, Kuma yasaan zasu Kara ciyar da kasuwar gab.
Haka zalika shugaban Kasuwar Sabon Gari, alhaji Abdulkadir B. Hussain ya hallacin wajen zaben, inda ya yaba da yadda kungiyar take gudanar da zabe lokaci bayan lokaci domin zaben wanda suka can can ta su tafiyar da al’amuran wannan kungiya.