Connect with us

News

Yan Sanda Sun Kama Mutum 15 Da Ake Zargi Da Fasa Rumbun Ajiye Kayan Abinci

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Rundunar ‘yansanda a birnin tarayya Abuja, ta ce ta kama wasu mutane 15 da ake zargi da lalata wani rumbun ajiyar kaya na hukumar raya babban birnin tarayya Abuja.

Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sanda a birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi a Abuja.

Ramadan: Sarkin Kano Ya Bukaci ‘Yan Kasuwa Da Su Rage Farashin Kayan Abinci  

Ta ce, wasu jami’an tsaro biyu da jami’an kula da rumbunan da ke aiki a wurin suna daga cikin wadanda ake zargin kan barna a rumbun ajiyar da ke unguwar Tasha a Abuja.

Adeh ta ce an kwato buhunan masara guda 26 da Babura biyar da kuma wasu kwanukan rufi na aluminium daga hannun wadanda ake zargin.

“Rundunar ‘yansanda a birnin tarayya Abuja ta samu rahoto game da harin da aka kai a unguwar Tasha da ke Abuja, a ranar 3 ga Maris.

Advertisement

“Harin ya haifar da barna tare da wawashe kayan ajiyar da ke wurin

Leadership ta ruwaito cewa sashen bunkasa noma da raya karkara na FCTA, ya tabbatar da sace kaya a ma’ajiyar a ranar Lahadi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending