Connect with us

News

Majalisar Wakilai Na Ƙoƙarin Yin Dokar Baiwa Masu Takaba Hutun Watanni Biyar

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Wani ƙudirin doka da ke neman a dinga bai wa masu takaba hutun watanni biyar ya yi nasarar tsallake karatu na biyu a zauren majalisar wakilan ƙasar nan.

Advertisement

Ɗan majalisa Saidu Abdullahi ne ya samar da ƙudurin don a dinga bai wa mata da maza da abokan zamansu suka rasu isasshen lokacin yin alhini da kuma samun damar shirya wa ƙalubalen da ke gaba, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya rawaito.

Shugaba Tinubu ya nemi ƴan majalisar wakilai su daina yawan kiran ministoci, su bar su yi aikinsu

Honorabul Saidu ya ce akwai buƙatar yin la’akari da ƙudurin saboda dalilai na addini da al’ada.

Advertisement

Ya ce an tsara wannan ƙudirin ne domin sanya Nijeriya a jerin kasashen da ke kan gaba a fannin walwalar ma’aikata kasancewar akwai dokar a kasashe da dama.

A cewarsa, binciken da aka gudanar ya nuna cewa a Nijeriya, hukumomi da ma’aikatun gwamnati kan ba da hutun kwanaki 14 ne kawai ga ma’aikatan da abokan zamansu.

Advertisement

Sai dai ya ce kwanaki 14 sunyi kadan idan aka yi duba da yanayin al’adu da addini a Nijeriya.

Shugaban majalisar, Tajudeen Abbas ya miƙa ƙudurin ga Kwamitin Sauye-Sauyen Bangarorin da suka shafi Jama’a don ƙara nazari.

Advertisement

Wasu addinan sun tanadi tsawon lokacin da ya kamata masu takaba su yi kafin komawa harkokinsu na yau da kullum. Alal misali a Musulunci, ana so mace ta yi takabar rasuwar mijinta har tsawon wata huɗu da kwana 10.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending