News
Hukumar EFCC Ta Sake Gurfanar Da Tsohon Gwamna, Dansa Bisa Zargin Almundahanar Naira Biliyan 29 A Gaban Kotu
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta sake gurfanar da tsohon gwamna Murtala Nyako da dansa Abdulaziz a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja ranar Alhamis bisa zargin almundahanar Naira biliyan 29.
An sake gurfanar da su a gaban kuliya bisa laifuka 37 da ake zargin sun aikata a lokacin da Mista Nyako ke gwamnan Adamawa.
Majalisar Wakilai Na Ƙoƙarin Yin Dokar Baiwa Masu Takaba Hutun Watanni Biyar
Sauran wadanda aka gurfanar dasu akwai Zulkifik Abba da Abubakar Aliyu.
Kamfanonin da ake zargin sun yi amfani da su wajen karkatar da kudaden—Blue Opal Limited, Sebore Farms & Extension Limited, Pagoda Fortunes Limited, Tower Assets Management Limited, da Crust Energy Limited — sun kasance gudaa biyar zuwa na tara.
Hukumar EFCC na tuhumar Mista Nyako, da dansa, da sauran wadanda ake tuhuma bisa zargin almundahanar kudi Naira biliyan 29.
EFCC ta yi zargin cewa wadanda ake tuhumar sun karkatar da kudade daga baitul malin Adamawa tsakanin watan Janairun 2011 zuwa Disamba 2014.
(NAN)
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
