News
Cutar Mashako ta kashe yara hudu a Kano
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
An samu bullar cutar Mashako yayin da ta kashe yara hudu a kauyukan karamar hukumar Mingibir ta jihar Kano.
Wata sanarwa da jami’in yada labarai na karamar hukumar Tasiu Yahaya Dadin-Duniya ya fitar, wanda aka turawa da gidan rediyon Arewa.
A cewar sanarwar “Yara hudu ne suka mutu sakamakon cutar Mashako sannan kuma yara 28 sun kamu da cutar a kauyukan Kwarkiya, Kuru, Kunya da Minjibir dake karamar hukumar Minjibir ta jihar Kano.
“Jami’in riko na karamar hukumar, Muhammad Yakubu Kunya, ya yi kira ga hukumomi da masu ruwa da tsaki da su gaggauta kai wa karamar hukumar Minjibir dauki domin kare lafiyar al’umma”.
Sanarwar ta ce Hakimin Karamar Hukumar ya kuma bukaci sarakunan gargajiya da malaman addinin Islama a cikin al’umma da su tashi tsaye wajen wayar da kan al’umma tare da yin addu’ar samun sauki.
A halin da ake ciki, ma’aikatar lafiya ta jihar ba ta tabbatar ko musanta bullar cutar ba.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
