Connect with us

News

Cutar Mashako Tayi  Sanadiyar Mutuwar Mutum 40 Bayan Sake Ɓulla A Kano

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Sabuwar annobar cutar Mashako  da ta ɓarke a jihar Kano ta laƙume rayukan fiye da mutane 40 yayinda wasu gommai yanzu haka ke kwance a asibitoci don karɓar kulawa bayan harbuwa da cutar.

Advertisement

Jaridar DAILY TRUST ta ruwaito yadda wakilinta ya ganewa idonsa cikar asibitin kula da cutuka masu yaɗuwa na jihar Kano da ake kira IDH ko kuma ‘zana’ maƙil da waɗanda suka harbu da cutar.

Wani jami’in asibitin da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar mata da yawaitar mutuwar da ake gani kullu yaumin sanadiyyar cutar Mashako a cikin asibitin na Zana ko kuma IDH.

Advertisement

Bayanai sun ce har zuwa tsakar ranar jiya anga dandazon marasa lafiyar da ke son ganin likita a asibitin na Zana sakamakon alamomin cutar Mashako

Rahotanni sun ce makwanni biyu kenan a jere ana ganin ƙaruwar masu fama da wannan Cutar Mashako da kan riƙe maƙogwaro tare da haddasa zazzabi da kuma ƙuraje a baki ko ɗaɗewar harshe da sauyawar kalar ido.

Advertisement

Wasu majiyoyi sun ce rashin kayakin aiki dama ƙwararrun likitocin da ke duba wannan cuta a sassan jihar shi ne ya haddasa cunkoson jama’a a asibitin wanda ke tsakar birnin Kano.

Tuni dai masu ruwa da tsaki suka ɗaura ɗamarar fara aikin wayar da kan jama’a game da alamomin cutar Mashako da kuma yadda za a baiwa kai kariya daga harbuwa da ita, lura da kasancewar cutar ta diphtheria a sahun cutukan da wani kan gogawa wani.

Advertisement

Alƙaluma sun nuna cewa wannan cuta ta fi illa ga ƙananan yara ta yadda ta ke farowa kamar mura gabanin tsananta tare da haddasa asarar rayuka.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending