Connect with us

News

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadiyar Mutuwar Mutane 179 A Najeriya  —Hukumar NEMA

Published

on

images (8)

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Hukumar Agajin Gaggauwa ta Najeriya NEMA ta ce adadin mutanen da ambaliyar ruwa tayi sanadiyar mutuwar su a jahohi 15 na Najeriya ya kai 179, yayin da ambaaliyar ta shafi akalla mutane dubu 208,655 a jahohi 22.

A Alhamis ɗin nan ne dai Hukumar NEMA ta bayyana halin da ake ciki game da irin ta’adin da ambaliyar ruwa ta haifar a sassan Najeriya, inda ta ce akalla kadada dubu 107,652 ta shafe, ta kuma lalata gidaje dubu 80,049.

Cutar Mashako Tayi  Sanadiyar Mutuwar Mutum 40 Bayan Sake Ɓulla A Kano

Daga cikin jahohin da iftila’in ya shafa akwai jihar Ribas da Neja da Benue da kuma jahohin da dama da ke ke yankin arewacin Najeriya.

Akalla ƙananan hukumomi 137 daga jahohi 28 ne ambaliyar ruwan bana ta shafa kamar yadda hukumar ta bayyana.

A ziyarar da kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila ya kai ofishin Hukumar NEMA, Darekta Janar na hukumar, Zubaida Umar, ta ce NEMA ta gudanar da bincike a kusan dukannin jahohin ƙasar dangane da iftila’in, sannan ta ƙara da cewa rashin samun tallafin kuɗi ne babbar matsalar da ke shafar aikin hukumar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending