News
Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano tare da hadin gwiwar BAN sun shirya taron wayar da kan ‘yan jaridu a kan cutar mashako
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Sakamakon yadda ake yada labaran karya game da cutar mashako, Ma’aikatar Lafiya ta jihar Kano tare da hadin gwiwar Breakthrough Action Nigeria (BAN) sun shirya taron wayar da kan ‘yan jaridu na tsawon kwanaki 2 kan cutar mashako, wadanda aka zabo daga gidajen rediyo daban-daban na jihar Kano.
Da yake jawabi a wajen taron bitar da aka gudanar a jihar Jigawa, Kwamishinan Lafiya na jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya bayyana cewa ma’aikatarsa na aiki ba dare ba rana na tsawon watanni goma sha daya domin ganin an dakile barkewar cutar mashako a jihar tare da tallafin gwamnatin jihar da kungiyoyin ba da tallafi da sauransu.
Harin Bama-Bamai Kan Masu Maulidi A Kaduna Ya Fusata ‘Yan Najeriya
Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da Jami’in yada labarai na Ma’aikatar Lafiya ta jihar Kano Ibrahim Abdullahi ya turawa da Jaridar Inda Ranka.
Dakta Labaran ya bayyana cewa, dole a yaba da rawar da kafafen yada labarai ke takawa wajen yaki da cutar mashako, inda ya bukaci mahalarta taron da su ba da goyon baya tare da hada kai da gwamnati don durkusar da cutar mashako ta hanyar samar da sahihan bayanai masu inganci.
Ya kuma yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa jajircewarsa na tallafawa ayyuka daban-daban kan harkokin kiwon lafiya da nufin ganin al’ummar jihar cikin koshin lafiya.
Kwamishinan wanda ya kuma yaba wa Gwamnan bisa yadda ya nuna kwazonsa wajen mayar da daukacin tsarin kiwon lafiya na jihar zuwa ga kololuwa, ya jaddada cewa makasudin taron shi ne kara fadakarwa da wayar da kan al’umma kan manyan alamomin cutar mashako ta hanyar shirye-shiryen rediyo daban-daban.
Dakta Labaran wanda ya samu wakilcin Malamin Kiwon Lafiya na Jihar Shehu Dabo, ya bayyana cewa rediyo ita ce hanya mafi sauki wajen isar da miliyoyin jama’a a lokaci daya, yana mai tabbatar da cewa mahalartan, a karshen taron, za su fahimci muhimmancin bayanan da za su sanar da jama’a game da cutar mashako.
Kwamishinan ya bukace su da su rinka gayyaci kwararrun da suka cancanta wadanda suke da isasshen ilimin da ake bukata a kan cutar mashako domin tattaunawa saboda kaucewa gurbatattun bayanai da ka iya kawo cikas ga yaki da cutar, duba da yadda Kano ce jihar da ta fi fama da cutar a fadin kasar nan.
Shi ma da yake nasa jawabin, jagoran Breakthrough Action Nigeria a jihar Kano, Ahmad Mu’az, ya ce BAN na ba da tallafi a kan lafiyar mata, jarirai da yara, tsarin iyali, abinci mai gina jiki, zazzabin cizon sauro, tarin fuka, Covid-19 da dai sauransu tare da mayar da kananan hukumomi, jiha da kasa baki daya a mahangarsu ta gudanar da aiki.
Ya kara da cewa, BAN na bayar da tallafi ga barkewar annoba a matakin kasa da jihohi, tare da yin aiki tare da gwamnati da kungiyoyin bayar da tallafi da kuma abokan aiki, inda ya kara da cewa a halin yanzu suna bayar da gudummawar fitar da bayanan da suka kamata da kuma shigo da al’umma don hannu wajen dakile barkewar cutar mashako a matakin kasa da kuma jihohin Kano da Bauchi.
