News
Harin Bama-Bamai Kan Masu Maulidi A Kaduna Ya Fusata ‘Yan Najeriya
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
An shiga rudani da kuma Makoki a ranar Litinin kan harin bam da sojojin Najeriya suka kai a Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna a ranar Lahadi, wanda ya yi sanadin mutuwar Mutanen kauyen 85.
Mazauna garuruwan da abin ya shafa sun ce suna gudanar da Maulidi ne, lokacin da sojoji suka jefa bama-baman, al’amarin da ya jawo Allah wadai a cikin gida da waje.
Gwamnatin Tarayya ta ce ta dauki nauyin wakilai 422 ne kawai daga cikin ‘yan Najeriya dubu 1 da 411
Mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Hadiza Balarabe ta ziyarci malaman addinin musulunci a jihar domin kwantar da tarzoma, yayinda yadda gwamnan jihar, Sanata Uba Sani, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan tashin bam din.
Kungiyar Kiristocin Najeriya da Kungiyar matasan Arewa da kungiyar kare hakki ta Human Rights Watch, da Amnesty International, da dai sauransu, sun yi Allah wadai da hare-haren bama-bamai da sojoji kaiwa.
A wani labarin kuma Gwamnatin Tarayya ta ce ta dauki nauyin wakilai 422 ne kawai daga cikin ‘yan Najeriya dubu 1 da 411
Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Kaduna ta ce aƙalla mutum 85 ne, kawo yanzu, aka tabbatar sun mutu a harin da aka kai jihar.
Ofishin hukumar na Arewa maso yamma ya samu bayanai daga hukumomin yankin cewa tuni aka yi jana’izar mutanen da suka rasu, ana kuma ci gaba da yin bincike.
Tun farko dai rundunar sojin saman ƙasar ta musanta hannu a kai harin.
A jiya Litinin ne, Majalisar Dattawan Najeriya ta lashi takobin gudanar da bincike kan harin kuskuren da rundunar sojin kasar ta kai, da ya janyo asarar rayuka.
Harin dai ya faru ne yayin da mutanen ke tsaka da taron Mauludi da suke yi duk shekara.
