News
Najeriya ta zama fagen kashe-kashe ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Tinubu – Atiku Abubakar
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya miƙa ta’aziyyarsa ga mutanen wani ƙauye a ƙaramar hukumar Rafi da ke jihar Neja, kan wani hari da ‘yan bindiga suka kai wanda ya yi ajalin wani mai rike da sarautar gargajiya.
A cikin makon nan ne yan bindiga suka afka kauyen cikin adadi mai yawa suka kashe aƙalla mutum 21 cikin har da wani jagora a kauyen, kuma suka danna kai cikin kasuwar Madaka a yammacin Alhamis.
Rahotanni na nuni da cewa maharan sun kai hari kasuwar ne da misalin ƙarfe 3 na yamma lokacin da ake tsaka da cin kasuwar, suka fara harbi kan mai uwa da wabi.
Cikin waɗanda aka kashe har da wani mahauci da ya yi aure ba tare da jimawa ba.
Bbc hausa ta ruwaito cewa da yake nuna bacin ransa kan abubuwan da suke faruwa a Najeriya Atiku Abubkar ya wallafa a shafinsa na X a ranar Juma’a ya ce Najeriya ta zama “fagen kashe-kashe” a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu.
Ya yi kira da a gaggauta kaddamar da ‘yansandan jihohi.
Ya ce “abin takaici ne yadda Najeriya ke zama fagen kashe-kashe. Kisan da aka yi na mutane da dama a ranar Alhamis, ciki har da wani shugaban ƙauye tare da sace mutane masu yawa a Madaka, a ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja, hakan na nuna abin da ake fada daban abin da ake aiwatarwa daban.
“Ya kamata mu baiwa bangaren tsaro muhimmanci kuma a gaggauta garambawul ga kundin mulki ta yadda za a kaddamar da ‘yansandan jiha kuma kauyuka a matakansu za su iya samar da tsaron da zai yi daidai da su,” in ji Atiku.
A watan Maris ɗin nan dai ayyukan ‘yan bindiga kama daga hare-hare da sace-sace na ƙara ta’azzara a wasu yankuna a arewacin Najeriya, ko da yake hukumomi na cewa suna iya kokarinsu wajen dakile hakan.
