News
Mutane da dama sun mutu sakamakon harin ‘yan bindiga a Neja
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wasu ‘yan bindiga sun kashe akalla mutane 21 a jihar Neja da ke yankin Arewa maso yammacin Najeriya, a wani hari da aka kai a wata kasuwa mai cunkoson jama’a. Wannan harin ya biyo bayan garkuwa da jama’a da aka yi a wannan wata da kuma sace tarin ‘yan makaranta a jihar Kaduna.
Wani basarake Alhaji Isah Bawale da kuma al’ummar karkarar Madaka sun bayyana wa kanfanin dillancin labaran Reuters cewar ‘yan bindiga sun shiga kasuwar a ranar Alhamis tare da bude wuta, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama. Sannan sun kara da cewa hukumomi na ci gaba da tattara bayanai game da wadanda suka mutu da wadanda suka bace.
Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Neja Bello Abdullahi Mohammed ya tabbatar da harin, amma bai bayar da cikakkun bayanai. Satar mutane don neman kudin fansane neman zama ruwan dare a arewacin Najeriya.
Advertisements
-
News4 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News4 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
-
News1 day ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
